Makiyaya sun kashe zakuna har shida don ceton shanunsu
- Wasu makiyaya sun sun sanya wa zakuna guba a ruwa don su kashe su
- A kasar Kenya ne abin ya faru inda makiyayan kan shiga har Tanzaniya don kiwo
- Dama dai a kasashen yankin akwai masu kiwon shanu suma
Wasu masu kiwon shanu a kasar Kenya wadanda ake kira Masai, masu zubi irin na fulanin Afirka ta yamma, sun kashe zakuna har shidda saboda suna musu dauki dai-dai kan dabbobinsu a kasar Tanzaniya mai makwabtaka.
Kamar yadda a Najeriya da sauran kasashen yammacin Afirka ake rigima da makiyaya da manoma, a can ma gabashin Afirka suna samun irin wannan matsala. Wannan karon kuma, an samu ne tsakanin masu kare hakkin dabbobi na gandun daji da makiyayan.
Su dai makiyayan, suna rangadi a dazukan yankin, inda sukan fuskanci hare-hare daga namun daji wadanda ke dauka abinci aka aiko musu, koo kuma farautar daji suke yi. Hakann kan jawo assarar rayuka da dabbobinsu.
DUBA WANNAN: Buhari ya yashe kogin Kwara kamar yadda Yaraduwa yayi
Masu kula da gandun dajin, sun tsinci gawarwakin garrken zakunan ne har su shidda, wadanda suka sha guba a ruwa suka mutu, abin takaici da babbar asara inji sojan gonar mai kula da ganndun dajin, wanda kuma ya ta'allaka wannan mugun aikin ga makiyaya masu yawo da shanu a yankin.
Su dai masu yawon bude ido sukan zo wannan yanki duk shekara su dauki hotuna, kuma suna samarwa kasashen Kenyar da Tanzaniya kudaden shiga.
Kisan naun daji da farauta ba bisa ka'ida ba, babban laii ne a duk kasashen duniya, musamman ga dabbobin da yawansu ya ragu matuka a dazuka.
Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng