Yaki da Ta'addanci: Tukur Buratai na ziyarar aiki a dajin Sambisa, yace a kamo masa Shekau

Yaki da Ta'addanci: Tukur Buratai na ziyarar aiki a dajin Sambisa, yace a kamo masa Shekau

- An gama da Boko haram a dajin Sambisa

- Shekau ya gudu Kamaru da shigar mata

- Buratai ya kai zuyara ga sojojin sa

Yaki da Ta'addanci: Tukur Buratai na ziyarar aiki a dajin Sambisa
Yaki da Ta'addanci: Tukur Buratai na ziyarar aiki a dajin Sambisa

A kokarin kakkabe burbushin mayakan ta'addanci na Boko Haram, Janar Tukur Buratai ya kai ziyaarar aiki ga sojojinsa na dajin Sambisa, inji shafin facebook na Sani Kuka-Sheka, kakakin sojojin.

A jiya Asabar ne ya kai ziyarar inda GOC 7 DIV Janar IM Yusuf da IM Obot na Operation Lafiya Dole suka kai masa ziyara.

Ya gana da mayakan sojn wadanda suka kame Kamp Zairo na yan ta'adda. Ya kuma ce nan gaba kadan zasu kawo karshen yakin baki dayansa.

Janar Buratai din, yace dole sojojin su kamo masa Shekau, shugaban Boko Haram, ko da rai ko ba rai. Dama dai sojin sun sanya ladan N3m ga duk wanda ya tona dan ta'addar wanda ya shafe shekaru tara a boye.

DUBA WANNAN: Budaddiyar Wasika zuwa ga shugaba Buhari

A yanzu dai an kame duk wasu manyan sansanoni na Boko haram, sai dai ba'a cimma kame shuggaban mayakan ba watau Abubakar Shekau, wanda ake sa rai ya tsere zuwa Kolofata a Kamaru.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng