Jirgi ya yi hatsari da fasinja 60 a Iran

Jirgi ya yi hatsari da fasinja 60 a Iran

- Mutane 60 sun mutu a kasar Iran yayin da wani jirgin sama yayi hatsari

- Jirgin saman da yayi hatsari a kasar Iran ya fado ne yankin Zagros mai cike da tsaunuka

Wani jirgin saman fasinja samfurin ATR 72-500 dauke da mutane 60 yayi hatsari a kasar Iran a ranar Lahadi

Jirgin ya fado ne a yankin Zagros mai cike da tsaunuka a lardin Isfahan a lokacin da yake kan hanyarsa daga birninTehran zuwa birnin Yasuj dake kudu maso yammacin kasar Iran.

"An sanya dukkan hukumomin bayar da agajin gaggawa cikin shirin ko-ta-kwana," in ji wani jami'in hukumar bayar da agaji.

Jirgi ya yi hatsari da fasinja 60 a Iran
Jirgi ya yi hatsari da fasinja 60 a Iran

Rashin yanayi mai kyau ya hana wani jirgi mai sukar ungulu da ke kai agajin gaggawa zuwa wurin da lamarin ya faru.

KU KARANTA : 2019: Buhari zai ci gaba – Inji babban sakataren gwamnatin tarayya

Har yanzu hukumomin kasar Iran bas u ce komai ba game da mutanen da suka yi hatsari a cikin jirgin

Rahotanni sun nuna cewa fasinjoji 60 ke cikins jirgin sai matuka biyu da kuma ma'aikatan sa biyu.

Idan aka tuna baya Legit.ng ta rawaito labarin yadda wani jirgi sama yayi hatsari a kasar Rasha jim kada bayan ya tashi daga filin jirgin saman birnin Moscow a makon da ya gabata.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng