Kamata yayi Buhari yayi koyi da 'Yar'adua ya cigaba da yashe Kogin Neja domin bunkasa tattalin arziki - Bahijja Mahmud
- An yi kira ga shugaba Muhammadu Buhari da ya cigaba da yashe kogin Neja
- Hajiya Bahijja Mahmud 'yar takarar gwamnan jihar Bauchi ita ce ta yi wannan kiran
- Ta bukaci shugaban da ya cigaba da aikin domin kawo cigaba ga yankin arewa
An yi kira ga shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya taimaki mutanen arewacin Najeriya ta hanyar cigaba da yashe kogin Neja, don bunkasa tattalin arzikin yankin arewa, ta hanyar sufuri da noma, kamar yadda tsohon shugaban kasa Marigayi Umaru Musa Yar'adua ya niyyar yi a lokacin da ya ke mulki.
'Yar takarar gwamnan Jihar Bauchi a karkashin jam'iyyar Green Party of Nigeria (GPN), Hajiya Bahijja Mahmood, ita ce ta yi wannan kira cikin hirar da tayi da manema labarai a Bauchi. Inda ta ce gwamnatin Umaru Musa ta bada himma kan wannan aiki na jawo ruwan teku zuwa arewa, amma tsohuwar gwamnatin Goodluck Jonathan tana hawa aka dakatar da aikin. Don haka yanzu ya kamata a cigaba da aikin.
DUBA WANNAN: Siyasar 2019: A mika mulki ga kabilar Igbo, inji Balarabe Musa
Bahijja Mahmud ta bayyana cewa wannan aikin shine zai taimaki arewa sosai wajen ciyar da yankin gaba a fannin samar da ayyuka ga matasa da wadata yankin da abinci da samar da arziki a fannin rayuwa. Amma abin takaici ne ace dan arewa yana mulki har ya zuwa wannan lokacin aikin yana tsaye ba a cigaba da shi ba.
Ta kara da cewa dukkan yankunan da ke da mashigan ruwa na teku a duniya sunfi yankunan da basu da ruwa cigaba, kuma komai dadewa akwai yiwuwar Najeriya zata iya rabuwa. Don haka idan akwai irin wannan mashiga ko hanyar ruwa to matsalar dan arewa zata zama da sauki a fannin bunkasar tattalin arzikin kasa. Don haka ta roki shugaba Buhari da ya taimaki 'yan baya a inganta rayuwar su, idan anyi wannan aikin dukkanin mutanen arewa da ke raye za su cigaba da samun ingancin rayuwa.
Haka zalika Bahijja Mahmud ta shawarci Yan Arewa da ke rike da madafun iko a wannan gwamnati kan su himmatu wajen taimakon 'Yan uwansu da inganta daukar matasa aiki tun daga matsayi na kasa har zuwa sama, domin arzikin mutanen Arewa ya inganta, musamman a wannan Lokaci da talauci ya addabi mutanen arewa, kuma duk harkokin da ake yi yanzu sun koma baya, aikata laifuka ya zama ruwan dare lamarin da idan ya cigaba tarbiyyar manyan gobe za ta ci gaba da gurbacewa ta yadda za a gamu da cikas wajen gina yankin da ciyar da arewa gaba kamar yadda wasu sassan kasar suka yi zarra ta fannin ci gaba da bunkasar tattalin arzikin mutanen wannan yanki.
Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng