'Yan majalisar Buhari dake hanƙoron kujerar gwamna a jihohin su

'Yan majalisar Buhari dake hanƙoron kujerar gwamna a jihohin su

A yayin da iska kaɗa ganye tare da guguwar siyasa take ci gaba da kaɗawa, wasu daga cikin 'yan majalisa da ministocin shugaban ƙasa Muhammadu Buhari, sun ɗaura ɗamarar tare da ɗaukan sulke na yakin neman kujerun iko a zaben 2019.

Rahotanni sun bayyana cewa, wannan yaƙin na neman madafun iko ba zai iyakance iya Abuja da fadar shugaban ƙasa ta Villa ba, domin kuwa za a miƙa shi zuwa jihohi inda suke neman ƙwacen kujerun wasu gwamnoni daga jihar Ekiti zuwa Akwa Ibom da kuma Abia zuwa...

Shugaba Buhari
Shugaba Buhari

Binciken jaridar The Nation ya bayyana cewa, mayaƙan na Buhari dake yunƙurin gusawa baya domin jagorantar jihohin su a zaben 2019 sun hadar da;

1. Ministan Tsaro; Mansur Dan-Ali - Jihar Zamfara

2. Karamin ministan man fetur; Ibe Kachukwu - Jihar Delta

3. Marcus Gundiri - Jihar Adamawa.

4. Obong Umana Umana - Jihar Akwa Ibom.

5. Nyerere Chinenye Anyim; Mataimakin shugaban jam'iyyar APC reshen Kudu maso Gabas - Jihar Abia.

KARANTA KUMA: Obanikoro ya yi murnar sauya sheƙa ta ɗan sa zuwa APC

6. Karamin ministan makamashi, ayyuka da gidaje; Suleiman Hassan - Jihar Gombe.

7. Ministan Sadarwa; Adebayo Shittu - Jihar Oyo.

8. Ministan harkokin mata; Aisha Alhassan - Jihar Taraba.

9. Babafemi Ojudu - Jihar Ekiti

10. Shugaban ma'aikatar NIMASA (Nigerian Maritime Administration and Safety Agency); Dakuku Peterside - Jihar Ribas.

11. Isima Ekere; Shugaban ma'aikatar NDDC - Jihar Akwa Ibom

12. Kayode Fayemi; Ministan albarkatun kasa - Jihar Ekiti

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel