Rungunar 'yan sanda ta bankaɗo wani kogon ƙungiyar shan jini tare da ƙaburbura a jihar Osun

Rungunar 'yan sanda ta bankaɗo wani kogon ƙungiyar shan jini tare da ƙaburbura a jihar Osun

Mazauna garin Ilobu na jihar Osun sun razana a yayin da jami'an tsaro na hukumar 'yan sanda ta jihar suka bankaɗo wani kogo na ƙungiyar shan jini tattare da ƙaburbura masu zurfi.

A ranar Juma'ar da ta gabata ne, hukumar 'yan sandan da jagorancin kwamishinan 'yan sandan jihar, Mista Fimihan Adeoye, ta bankaɗo wannan kogo a cikin wani babban gida dake yankin Molete na garin Ilobu.

Rungunar 'yan sanda ta bankaɗo wani kogon ƙungiyar shan jini tare da ƙaburbura a jihar Osun
Rungunar 'yan sanda ta bankaɗo wani kogon ƙungiyar shan jini tare da ƙaburbura a jihar Osun

Kwamishinan 'yan sandan ya shaidawa manema labarai cewa, sun samu nasarar cafke mutane biyu 'yan uwan juna a yayin bankado wannan kogo.

KARANTA KUMA: Rikicin APC ya ƙara zufafawa, taron dangi akan tsige Oyegun ya yi ƙarfi...

Legit.ng da sanadin jaridar The Punch ta ruwaito cewa, shugaban wannan kungiya ta asiri ya shiga rububi, inda jami'an tsaro suka bazama wajen damkar sa tare da duk wani dake alaka da kogon.

Jaridar Legit.ng ta kuma ruwaito cewa, hukumar 'yan sanda ta cafke mutane 10 da laifin ƙone gidajen 'yan gudun hijira a jihar Nasarawa.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng