Siyasar 2019: A mika mulki ga kabilar Igbo, inji Balarabe Musa
- Alhaji Balarabe Musa tsohon dan siyasa ne, kuma tsohon gwamnan Kaduna
- Ya yi kira ga masu ruwa-da-tsakin siyasar kasar nan da su mika wa kabilar Ibo mulki a badi
- Suma dai kabilar ta Ibo, suna son su dana mulki, tunda basu taba yi ba
Tsohon gwamnan Kaduna, sannan kuma shugaban jam'iyyar Peoples Redemption Party (PRP), Alhaji Abdulkadir Balarabe Musa, ya bukaci da a mika shugabancin kasar nan ga al'ummar Igbo. A cikin hira da aka yi dashi ranar Asabar dinnan a Kaduna, Tsohon gwamnan ya ce hakan ya zama dole saboda an jima ana yaudarar al'ummar Igbo, kuma an yi watsi dasu a harkar shugabancin kasar nan na tsawon shekaru.
DUBA WANNAN: Wasika ga shugaba Buhari kan yaki da Boko Haram
Shugaban jam'iyyar PRP din, ya yi zargin cewa Hausawa da Yarabawa sune suke da alhakin rashin cigaban siyasar yankin Igbo.
Ya ce yana mamakin me yasa mutanen Najeriya suke shakkar bawa kabilar Igbo mulkin kasar nan, inda ya kara da cewar, duk kokarin da dattawan arewa ke yi na ganin sun tura nasu domin samun shugabancin kasar nan, su nayi ne kawai saboda cigaban kansu, ba wai suna yi bane saboda cigaban Najeriya.
Sannan ya kara da cewar, a duk kabilun kasar nan babu wanda suke da hadin kai da son ganin an zauna lafiya kamar kabilar Igbo, inda ya kara da cewar sun fi kowa kishin kasa, ba su taba nuna bambanci ba, sun kasance masu hadin kai, ba irin Hausawa da Yarabawa masu tsaurin ra'ayi ba.
Da jimawa kujerar shugaban kasa tana zagaya wa tsakanin al'ummar kasar nan, musamman ma a yankin arewa, amma har wayau al'ummar Igbo basu taba shugabancin kasar nan ba.
Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng