Duniya makaranta: Hotunan wata kyakkyawar macen soja ta shirya auren kanta da kanta

Duniya makaranta: Hotunan wata kyakkyawar macen soja ta shirya auren kanta da kanta

- Hotunan wata kyakkyawar macen soja ta shirya auren kanta da kanta

- Tabbas duniyar nan da muke ciki cike ta ke da abubuwan al'ajabi tare kuma da darussa da dama

- Shaunice Safford ta kara da cewa wannan ranar ba zata taba mancewa da ita ba don kuwa a ranar ne burin ta ya cika

Tabbas duniyar nan da muke ciki cike ta ke da abubuwan al'ajabi tare kuma da darussa da dama da ba mahalukin da ya taba kai karshen su har ya koma ga mahaliccin sa. Haka nan kuma abubuwan mamaki a kullum faruwa suke ta yi.

Duniya makaranta: Hotunan wata kyakkyawar macen soja ta shirya auren kanta da kanta
Duniya makaranta: Hotunan wata kyakkyawar macen soja ta shirya auren kanta da kanta

KU KARANTA: Obasanjo ya ce da ya kashe kan sa inda ya san Najeriya ba zata cigaba ba

Yau ma kuma gamu dauke da wani labarin ban al'ajabi, mamaki da kuma takaici ma a wajen wasu inda muka samu cewa wata kyakkyawar macen soja ta sha alwashin auren kan ta da kan ta.

Ita dai wannan macen mai suna Shaunice Safford tana kuma da adreshin dandalin sada zumunta na Instagram ne (@drsafford) inda ta kudruri aniyar cigaba da wanzar da rayuwar ta tare da ita kanta din bayan auren da ta yi.

A cewar ta, Macen sojan Shaunice Safford ta bayyana cewa ba tun yanzu ba ta dade tana muradin ranar da zata yi aure ta zauna cikin kwanciyar hankali da lumana amma hakan bai samu ba sai a ranar 14 ga wannan watan da muke ciki.

Shaunice Safford ta kara da cewa wannan ranar ba zata taba mancewa da ita ba don kuwa a ranar ne burin ta ya cika kuma rayuwar ta ta kammala cika da farin ciki da jin dadi, hade da walwala.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng