Jam'iyyun siyasar Najeriya zasu sami gudummawar N2b daga Amurka don bunkasa dimokuradiyya
- Akwai jam'iyyun siyasa masu rajista 67 a yanzu a Najeriya
- Manyan jam'iyyun dai basu wuce biyu zuwa uku ba
- Za'a raba musu dala miliyan biyar da rabi
Kungiyar International Republican Institute (IRI), mai kare muradun jamhuriyya da dimokuradiyya, ta bude gidauniyar tara dala miliyan biyar da digo biyar don jam'iyyun kasar nan su mora su kara armashi.
Za'a tara kudaden ne a shekaru biyar, kuma jam'iyyu masu rajista ne zasu mori kudin, fadin daraktan cibiyar wadda zata yi aikin a Najeriya, Sentell Bernes, karkashin shirin Responsive Political Party Program (RPPP) na Amurkar, a Abuja a jiya.
DUBA WANNAN: Budaddiyar wasika zuwa ga shugaba Buhari
Jakadan Amurka da shugaban cibiyar ta IRI dai sun halarci bikin bude gidauniyar, kuma sun sha alwashin ciyar da dimokuradiyyar Najeriya gaba.
A cewar Mista Bernes, an zabi jihohi hudu da shirin zai fara dubawa da kudaden ta hannun USAID, hukumar bayar da agajin Amurka a kasashe mabukata, jihohin kuwa sune, Adamawa, Bauchi, Ebonyi da Sokoto.
Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng