Buhari yayi fatali da dokar kafa hukumarZaman lafiya ta Nigerian Peace Corps

Buhari yayi fatali da dokar kafa hukumarZaman lafiya ta Nigerian Peace Corps

- Buhari yayi fatali da dokar kafa hukumarZaman lafiya ta Nigerian Peace Corps

- Shugaban kasar ya dauki shawarar manyan makusantan sa da kuma jami'an tsaron kasar

- An kai wa shugaban kasar kudurin dokar tun a farkon watan Disembar shekarar bara

Yayin da ake ta cigaba da takaddama a tsakanin jami'an 'yan sandan Najeriya da kuma ma'aikatan kungiyar nan ta samar da zaman lafiya watau Nigerian Peace Corps game da babban ofishin ta dake a garin Abuja, yanzu kuma shugaban kasar ta Najeriya Muhammadu Buhari yayi fatali da batun sanyawa kudurin su hannu.

Buhari yayi fatali da dokar kafa hukumarZaman lafiya ta Nigerian Peace Corps
Buhari yayi fatali da dokar kafa hukumarZaman lafiya ta Nigerian Peace Corps

KU KARANTA: Ba mu da masaniya kan inda Shekau ya ke - Sojin Najeriya

Majiyar mu dai ta tattaro cewa da alama dai shugaban kasar ya dauki shawarar manyan makusantan sa da kuma jami'an tsaron kasar inda suke ganin a wannan lokacin da kasar ta ke ciki bata bukatar karin wasu jami'an tsaron na daban.

Legit.ng dai ta samu cewa an kai wa shugaban kasar kudurin dokar da zai tabbatar da su jami'an na Nigerian Peace Corps halattatu a Najeriya tun a farkon watan Disembar shekarar bara amma har kawo yanzu bai saka ma kudurin dokar hannu ba.

A wani labarin kuma, Fitaccen dan majalisar tarayyar Najeriya din nan kuma jigo a siyasar kasar a jamhuriya ta biyu, Dakta Junaid Mohammed ya yi Allah-wadai da yadda shugaban kasar Najeriya da kuma gwamnomin Arewa suke yi wa kashe-kashen da ake ta yiwa al'ummar arewa rikon sakainar kashi.

Dakta Junnaid, wanda kuma ke zaman daya daga cikin dattawan Arewa ya bayyana cewa abun takaici ne yadda bayan 'yan bindiga sun kashe mutane akalla 35 a jihar Zamfara, amma sai gwamnonin suka dunguma zuwa Katsina wajen shugaba Buhari suka kyale al'ummar ta su.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng