Gwamnonin APC 14 da suka gana da shugaba Buhari a garin Daura

Gwamnonin APC 14 da suka gana da shugaba Buhari a garin Daura

A ranar Juma'ar da ta gabata ne, gwamnonin jam'iyyar APC suka dirra a jihar Katsina domin mika ta'aziyyar su ga shugaban kasa Muhammadu Buhari, a mahaifar sa dake garin Daura sakamakon rashin da yayi a makon da ya gabata.

Gwamnonin APC 14 da suka gana da shugaba Buhari a garin Daura
Gwamnonin APC 14 da suka gana da shugaba Buhari a garin Daura

Gwamnonin APC 14 da suka gana da shugaba Buhari a garin Daura
Gwamnonin APC 14 da suka gana da shugaba Buhari a garin Daura

Bayan ganawar gwamnonin da shugaba Buhari, domin kawar da hasashe sun bayyana cewa ziyarar su ba ta da nasaba da zaben kasa na 2019 mai gabatowa.

Legit.ng ta fahimci cewa, gwamnonin APC 14 ne suka ziyarci shugaban a garin na Daura, inda uku basu samu damar halartar ba sai wakilai da suka tura.

Ga jerin sunyen gwamnonin 14 da suka ziyarci garin daura tare da jihohin da suke jagoranta.

1. Shugaban kungiyar gwamnonin Najeriya; Abdulaziz Abubakar Yari na jihar Zamfara.

2. Gwamna Rochas Okorocha na jihar Imo.

3. Gwamna Abubakar Muhammad na jihar Bauchi.

4. Gwamna Kashim Shettima na jihar Borno.

5. Gwamnan jihar Oyo, Abiola Ajimobi.

6. Aminu Bello Masari na jihar Katsina.

7. Mallam Nasir El-Rufa'i; gwamnan jihar Kaduna.

8. Gwamna Badaru Abubakar na jihar Jigawa.

9. Abdullahi Umar Ganduje; gwamnan jihar Kano.

10. Gwamna Godwin Obaseki na jihar Edo.

11. Yahaya Bello; gwamnan jihar Kogi.

12. Atiku Bagudu na jihar Kebbi.

13. Gwamna Abubakar Sani Bello na jihar Neja.

14. Umaru Tanko Al-Makura na jihar Nasarawa.

KARANTA KUMA: Kotu ta yanke hukuncin ɗauri na makonni 8 kan wani mutum da ya keta dokar zirga-zirga

Gwamnonin jihar Benuwe, Osun da kuma Ogun ba su samu halartar taron ba, inda mataimakan su suka wakilce su a gaban shugaban kasa. Sai kuma gwamnonin jihar Yobe da Filato da suka tura wasu jiga-jigan gwamnatin su domin wakilci.

Kamfanin dillancin labarai na Najeriya ya fahimci cewa, wannan ganawa ta gwamnonin APC ita ce makamanciya ta farko da ta gudana a wajen fadar shugaban kasa.

A yayin haka kuma, jaridar Legit.ng ta ruwaito cewa, gwamnan jihar Zamfara ya kausasa harshe kan hukumomin tsaro dangane da kisan gillar mutane 39 da ta afku a jihar sa.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng