Shugabannin APC, Tinubu za su gana da Buhari a Daura
A yau ne shugaban kasa Muhammadu Buhari, zai gana da Asiwaju Bola Ahmed Tinubu da sauran shugabannin jam'iyyar su ta APC a mahaifar sa ta garin Daura dake jihar Katsina.
Wannan ganawa tana zuwa ne bayan kwana guda da ganawar shugaban da gwamnoni jam'iyyar ta APC.
Kamfanin dillancin labarai na Najeriya ya ruwaito cewa, jiga-jigai da kusoshin jam'iyyar zasu hallara ne a garin Daura domin yiwa shugaban kasa ta'aziyar rashin 'yan uwan sa biyu a cikin makon da ya gabata.
Legit.ng ta fahimci cewa, Tinubu da Cif Bisi Akande, sun yi ganawar sirrance da shugaba Buhari a fadar sa ta Villa dake Abuja a ranar 13 ga watan Fabrairu.
Akande ya gana da manema labarai bayan ganawar su ta ranar Talata da shugaban kasar, inda ya yi watsi da hasashen cewa sun gana ne domin zaben kasa na 2019, ya kuma ce sun ziyarci fadar ne domin bayyana ta'aziyar su ga shugaba Buhari.
KARANTA KUMA: Kashe-Kashe: Hukumomin tsaro sun gaza a jihar Zamfara - Yari
A nasa ɓangaren, Tinubu ya bayyana tsayuwar sa wajen tabbatar da jam'iyyar APC ta yi nasara a dukkan kujerun ta na takara a zaben 2019.
Ya kuma yabawa shugaba Buhari da ya zabe sa a matsayin kanwa uwar gamin matsalolin jam'iyyar, wajen tuntube da sulhunta duk wani rikici domin samun hadin kai na tunkarar zaben.
Wata majiyar rahoto ta bayyana cewa, akwai yiwuwar ganawa ta biyu na shugaba Buhari da Tinubu a yau asabar ba zata tsaya iya ta'aziyya kadai ba.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:
https://facebook.com/naijcomhausa
https://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng