Kotu ta yanke hukuncin ɗauri na makonni 8 kan wani mutum da ya keta dokar zirga-zirga

Kotu ta yanke hukuncin ɗauri na makonni 8 kan wani mutum da ya keta dokar zirga-zirga

Wata kotu dake zamanta a unguwar Kubwa ta birnin Abuja, ta zartar da hukuncin ɗauri na makonni 8 kan wani mutum mai shekaru 53 a duniya, Ayuba Ibrahim, bisa laifin karan tsaye da ya yiwa dokokin zirga-zirga.

Kotun ta yanke masa wannan hukunci bisa laifin daukar fasinja a haramtaccen wuri, baya ga yin kabu-kabu da babur marar lasisi.

Kotu ta yanke hukuncin ɗauri na makonni 8 kan wani mutum da ya keta dokar zirga-zirga
Kotu ta yanke hukuncin ɗauri na makonni 8 kan wani mutum da ya keta dokar zirga-zirga

Sai dai kotun bisa ga adalci da kuma rangwami na mai shari'a Mohammed Marafa, ya bayar da zabi na biyan diyya ta N4000 tare da gargadin sa kan ya kasance mutum na gari.

KARANTA KUMA: Wata jam'iyya ta bukaci a yi watsi da zaben kananan hukumoni na jihar Kano

Idowu Lawal, jami'in dan sanda mai shigar da kara ya shaidawa kotun cewa, an cafke wanda ake zargi a unguwar Kubwa a ranar 14 ga watan Fabrairu, a yayin da yake sabawa sassa na 4, 36, 68, da kuma na 7 na dokokin zirga-zirga.

A yayin haka kuma, jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa, gwamnan Abdulaziz Yari na jihar Zamfara, ya kausasa harshe kan hukumomin tsaro dangane da kisan gillar mutane 39 a karamar hukumar Zurmi ta jihar sa.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng