Bera da ɓarna: Beraye sun tafka ma manoman shinkafa mummunar ta’asa a jihar Kebbi
Rahotanni sun tabbatar da cewa wasu guma guman beraye sun da kwari sun tafka ma manoman shinkafa mummunan asara a jihar Kebbi, kamar yadda BBC Hausa ta ruwaito.
Majiyar Legit.ng ta ruwaito tsabar munin ta’asan da berayen suka tafka a gonakan ya sa wasu manoman yin watsi da lamarin noman shinkafar ma gaba daya, inda suka ce babu riba idan suka cigaba a haka.
KU KARANTA: Raɗe raɗen komawar Kwankwaso PDP: Ko mutum shi ne shugaban shaiɗanu ba zamu bar masa PDP ba – Inji Shekarau
Wannan matsalar tafi kamari ne a yankunan Augie, Argungun, Bagudo, Danda, Kalgo da Bunza kuma sune yankunan da suka fi samar da shinka a Najeriya gaba daya, hakan ne ya sanya ake fargabar za’a iya fuskantar karin karancin shinkafa a Najeriya.
Wani manomi shinkafa da matsalar ta shafa a garin Argungu, Malam Sanusi Adamu ya bayyan ma majiyarmu cewar "Berayen sun yi wa kusan dukkanin manoman Argungu barna, da kuma kwari da ke lalata shinkafa hakan kum ya sabbaba raguwar nomar shinkafa.”
A nasu bangaren, ma’aikatar gona ta jihar Kebbi, ta bakn kwamishinan ma’aikatar, Alhaji Garva Dan Dika tun bayan samun labarin matsalar sun sayo magungunan da za’a yi ma gonaki feshi dasu, sune zasu kashe berayen da kwarin.
Idan za’a tuna, gwamnatin Najeriya karkashin jagorancin shugaban kasa Muhammadu Buhari ta dauki matakin haramta shigar da shinkafa don bunkasa nomar shinkafa a Najeriya, kuma jihar Kebbi na kan gaba wajen cika wannan kudiri na Buhari.
Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
ko a http://twitter.com/naijcomhausa
KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng