APC ta kara kaimi wajen hana Kwankwaso, Saraki da Ortom shekawa PDP
Shugaba Muhammadu Buhari da shugabancin jam’iyyar All Progressives Congress (APC) na aiki tukuru wajen dinke barakar da ke cikin jam’iyyar kafin a fara yakin neman zaben shekarar 2019.
Jam’iyyar ta kara kaimi wajen tabbatar da cewa shugaban majalisan dattawa, Abubakar Bukola Saraki; gwamnan jihar Benuwe, Samuel Ortom; da tsohon gwamnan jihar Kano, Sanata Rabiu Kwankwaso, basu canza shekara zuwa jam’iyyar adawa ta PDP ba.
Majiya mai karfi daga jam’iyyar APC ya bayyana cewa wannan shine babban dalilin da yasa shugaba Buhari ya nada kwamitin sulhu karkashin jagorancin babban jigon jam’iyyar kuma tsohon gwamnan jihar Legas, Asiwaju Bola Tinubu.
KU KARANTA: Badakalar bacewar kudi a JAMB: Shehu Sani ya bayar da mafita
A wani hira da jaridar Daily Independent ranan Laraba, wani mamban kwamitin ayyukan jam’iyyar ya ce shugaba Buhari ya yi kuzari wajen nada kwamitin sulhu da wuri kafin abubuwa su baci.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng