Dandalin Kannywood: Yaran wani jarumin fim sun yi barazanar kashe ni - Nura M. Inuwa

Dandalin Kannywood: Yaran wani jarumin fim sun yi barazanar kashe ni - Nura M. Inuwa

- Yaran wani jarumin fim sun yi barazanar kashe ni - Nura M. Inuwa

- Nura M. Inuwa ya yi wani dogon rubutu a shafin sa na dandalin sada zumunta na Instagram

- Mawakin ya dora hotunan sa tsaffi na shekarun baya kafin ya gamu da ibtila'i daga wasu mugaye

Fitaccen mawakin nan na fina-finan Hausa a masana'antar Kannywood watau Nura M. Inuwa ya yi wani dogon rubutu a shafin sa na dandalin sada zumunta na Instagram mai cike da ban tausayi inda yayi ikirarin cewa wani mutum da ya kira yaron wani jarumin Kannywood ya yi barazanar kashe shi.

Dandalin Kannywood: Yaran wani jarumin fim sun yi barazanar kashe ni - Nura M. Inuwa
Dandalin Kannywood: Yaran wani jarumin fim sun yi barazanar kashe ni - Nura M. Inuwa

KU KARANTA: Jahohi 11 sun sake karbar kudi a hannun Buhari

A cikin sakon da ya fitar, mawakin ya dora hotunan sa tsaffi na shekarun baya kafin ya gamu da ibtila'i daga wasu mugaye da suka watsa masa ruwan guba a fuskar sa da kuma yayi sanadiyyar lalacewar wani sashe na fuskar sa.

Legit.ng ta samu cewa mawakin ya labarta cewa yanzu yana dauke da sakon waya da daya daga cikin yaran wani jarumin kannywood ya turo masa inda yake cewa sai sun karasa aikinsu a kan shi kuma wai shege ka fasa a cewarsa.

Sai dai kuma mawakin ya bayyana cewa bai san ko waye ya turo masa sakon ba amma yasan da akwai sunan jarumin tunda kuma ya sha alwashin dora duka sakwannin da akayi masa da kuma lambar idan har suka cigaba.

Daga karshe kuma mawakin ya bayyana cewa yana mai shaida ma wanda ke turo masa sakon cewar shi Allah kawai yake tsoro ba wani mutum ba.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng