Kashedin ka da taba addinin Allah - Musulman Faransa sun fadawa shugaba Macron
- Kashedin ka da taba addinin Allah - Musulman Faransa sun fadawa shugaba Macron
- Wannan ya biyo bayan furucin shugaban kasar da ya yi baya na bukatar sa ta yin wasu sauye-sauye
- Ahmed Ogras ya bayyana cewa yin hakan zai zama tamkar takalar hancin su ne
Wani jagoran fafutukar kare musulunci da musulman kasar Faransa mai suna Ahmed Ogras ya jawo hankalin shugaban kasa mai suna Emmanuel Macron da kar ya kuskura ya nemi taba addinin Allah a kasar kasantuwar shi ne addini na biyu wajen yawa a kasar.
KU KARANTA: Jahohi 11 sun kara karbar kudi daga wajen Buhari
Kamar yadda muka samu, wannan kalaman dai sun biyo bayan furucin shugaban kasar da ya yi a kwanakin baya na bukatar sa ta yin wasu sauye-sauye a kan yadda ake gudanar da addinin musulunci a kasar da nufin kawo dai-daito.
Legit.ng ta samu cewa to sai dai jagoran na musulman kasar Ahmed Ogras ya bayyana cewa yin hakan zai zama tamkar takalar hancin su ne domin kuwa kowa zai iya tsayawa a matsayin sa ba tare da tsangwama ba.
A wani labarin kuma, Sabbin bayanai masu daure kai na cigaba da bayyana a zagaye da auren nan da ake sa ran daurawa a tsakanin diyar mataimakin shugaban kasa Farfesa Osinbajo mai suna Oluwadamilola Osinbajo ko kuma Kiki da angon ta mai suna Oluseun Bakare da ke zama da ga hamshakiyar mai kudin na Bola Shagaya.
Kamar yadda muke samu daga majiyoyin mu, a sabanin yadda labarin ya fara fita na cewa wanda zai aure diyar ta Osinbajo musulmi ne, yanzu kuma an gano cewa Kirista ne da yake aiki a cocin Redeemed Christian Church of God.
Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da
Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa
KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng