Shege-ka-fasa: Ba wanda ya isa ya yi wa Sanata Shehu Sani kiranye - Wasu matasa

Shege-ka-fasa: Ba wanda ya isa ya yi wa Sanata Shehu Sani kiranye - Wasu matasa

- Ba wanda ya isa ya yi wa Sanata Shehu Sani kiranye - Wasu matasa

- Shugaban kungiyar ta Youth Movement for Credibility in Kaduna State mai suna Mustapha Aliyu, ya bayyana hakan

- Matasan suka shawarci duk wani dan jin zafin Sanatan da ya yi hakuri ya dena

Wata kungiyar matasa ta yankin mazabar jihar Kaduna ta tsakiya a majalisar dattijai mai suna Youth Movement for Credibility in Kaduna State a turance ta yi kaca-kaca da wasu mutane da a baya suka sanar da kudurin su na fara shirin yi wa Sanata Shehu Sani kiranye daga majalisar dattijai.

Shege-ka-fasa: Ba wanda ya isa ya yi wa Sanata Shehu Sani kiranye - Wasu matasa
Shege-ka-fasa: Ba wanda ya isa ya yi wa Sanata Shehu Sani kiranye - Wasu matasa

KU KARANTA: Gobara ta halaka dalibi 1 a makarantar Sakandare ta Daura

Shugaban kungiyar ta Youth Movement for Credibility in Kaduna State mai suna Mustapha Aliyu, ya bayyana hakan ne a yayin wani taron manema labarai da ya kira a garin Kaduna inda ya bayyana cewa matasan suna jin zafin irin farin jin da Sanatan ke ta samu ne.

Legit.ng ta samu cewa daga nan ne kuma dai sai matasan suka shawarci duk wani dan jin zafin Sanatan da ya yi hakuri ya dena domin kuwa hakan ba zai tsinana masa komai ba.

A baya ma dai mun ruwaito maku cewa Sanatan nan dake wakiltar mazabar shiyyar dan majalisar dattijai ta Kaduna ta tsakiya watau Kwamnared Shehu Sani ya fito yayi wa wasu yan mazabar ta sa raddi game da yunkurin da suke yi na yi masa kiranye daga majalisar.

Sanatan wanda ya mayar masu da raddin a ta bakin mai magana da yawun Suleiman Ahmed ya bayyana 'yan kungiyar a matsayin marasa aikin yi da gwamnatin jihar karkashin jagorancin Gwamna El-Rufa'i ta dauka haya domin cimma wani buri na shi.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng