A shiga taitayi: Amaechi ya bayyana halin da Najeriya zata shiga muddin yan Najeriya basu zabi Buhari a 2019 ba
Ministan harkokin sufuri, Rotimi Amaechi ya bayyana cewa da zarar gwmanatin shugaban kasa Buhari ta fadi zabe a shekarar 2019, tabbas Najeriya za ta samu koma baya, cibayan da zai mayar damu shekaru 10 baya.
Amaechi ya bayyana haka ne a ranar Alhamis 15 ga watan Feburairu, a garin Abuja, inda yayi nudi da akwai bukatar APC ta maimaita shekaru hudu a karagar mulku, don cika alkawurran da ta daukan ma yan Najeriya.
KU KARANTA: AIki ga mai ƙare ka: EFCC na gab da ƙwaƙulo tsohon Ministan Jonathan daga kasar da yayi gudun hijira
The Cables ta ruwaito Amaechi na fadin gwamnatinsu ba gwamnatin ma’asumai bane, don haka akwai wuararen da suke tafka kura kurai, amma yana da tabbacin Buhari na yaki da rashawa haikan.
“Idan har muka fadi zabe, toh cigaban da Najeriya ta samu zai koma cibayan shekaru 10, saboda kurayen PDP na nan suna jira. Ina fata yan Najeriya basu manta cewar a lokacin da muka zo, mun tarar Gwamnatin Jonathan na cin bashi tana biyan albashi ne, amma yanzu ta sauya zani.” Inji shi.
Amaechi yace idan aka kwatanta farashin mai a zamanin Jonathan da na Buhari, ana siyar da gangar mai dala 110-120, amma a yanzu dala 50 ne zuwa 80, duk da haka ba’a taba fashin biyan albashi ba.
Majiyar Legit.ng ta ruwaito a lokacin yakin neman zaben 2015, Buhari ya taba kiran Amechi akan yadda zasu rage burukan da yan Najeriya suka daura akan gwmanatinsu, don haka ne yace ya san basu gama aiki ba, kuma zasu habbaka tattalin arziki.
Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
ko a http://twitter.com/naijcomhausa
KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng