Ladabin kunama: Yan Najeriya sun kaca-kaca da El-Rufa'i bisa yadda yake dukawa gaishe da Buhari
- Yan Najeriya sun kaca-kaca da El-Rufa'i bisa yadda yake dukawa gaishe da Buhari
- Sun ce hakan yayi ta yi wa tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar
- A jiya shugaba Buhari ya ziyarci jihar Kaduna ne inda ya kaddamar da wasu jiragen leken asiri marasa matuka
Biyo bayan wasu hotunan gwamnan jihar Kaduna da suka yi ta yawo a kafafen sadarwa a jiya da aka dauka yayin da ya duka har kasa wajen gaishe da shugaban kasa lokacin da ya isa jihar Kaduna suna cigaba da tayar da kura da kuma jawo mabambantan ra'ayoyi.
KU KARANTA: An yankewa wani dan Boko Haram shekaru 20 gidan yari
Wasu jama'a da dama dai na ganin irin wannan ladabin da gwamnan ke yi wa shugaba Buhari ko kusa bai kai zuci ba sannan kuma ba da gaske ya ke yi ba don kuwa a cewar su hakan yayi ta yi wa tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar kafin daga baya suyi baram-baram.
Legit.ng ta samu dai cewa a jiya shugaba Buhari ya ziyarci jihar Kaduna ne inda ya kaddamar da wasu jiragen leken asiri marasa matuka da rundunar tsaron Najeriya suka kera kafin daga bisani ya zarce mahaifar sa ta Daura.
A wani labarin kuma, Wata kungiyar matasa ta yankin mazabar jihar Kaduna ta tsakiya a majalisar dattijai mai suna Youth Movement for Credibility in Kaduna State a turance ta yi kaca-kaca da wasu mutane da a baya suka sanar da kudurin su na fara shirin yi wa Sanata Shehu Sani kiranye daga majalisar dattijai.
Shugaban kungiyar ta Youth Movement for Credibility in Kaduna State mai suna Mustapha Aliyu, ya bayyana hakan ne a yayin wani taron manema labarai da ya kira a garin Kaduna inda ya bayyana cewa matasan suna jin zafin irin farin jin da Sanatan ke ta samu ne.
Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da
Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa
KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng