Babu maraya sai rago: Karanta Labarin ‘Sani Coach’ wani gurgu dake koya ma masu ƙafa kwallon ƙafa

Babu maraya sai rago: Karanta Labarin ‘Sani Coach’ wani gurgu dake koya ma masu ƙafa kwallon ƙafa

Ikon Allah sai kallo, kuma dama ai muddin zuciyar mutum bata mutu ba, toh yana tare da nasara a duk abinda ya sa a gaba, yayin da kuma duk cikar halittar mutum, da zarar zuciyarsa ta mutu, toh shi ma matacce ne.

A nan wani matashi aka samu, mai nakasar gurgunta, Coach Sani a garin Jos na jihar Filato, wanda ya shahara wajen horas da matasa masu sha’awar kwallon kafa yadda zasu gwanance a wannan harka.

KU KARANTA: Yan Hisbah sun kai samame, sun damke mabarata guda 8 a cikin garin Kano

VOA Hausa ta ruwaito Caoch Sanin a fita ne a kowacce safiya zuwa filin kwallo dake tashar jirgin kasa a garin Jos don kulawa da yaransa, dake taka leda a kungiyarsa ta kwallon kafa daya assasa, mai suna Gimbiya Academy.

Kamar kowanne fannin rayuwa, Coach Sani yace shi ma yayi fama da wasu kalubale game da harkar da yasa a gaba, inda a gidansu aka nemi a hana shi buga kwallon gaba daya, amma daga bisani wani yayansa ya sa baki, yace a kyale shi, a yanzu haka Coach Sani ya kwashe sama da shekaru 20 yana buga kwallon guragu, kuma yana horas da yan wasa.

Dayake bayani game da nasarorin da ya samu a harkar kwallo, Coach Sani yace yana alfahari domin zuwa yanzu akwai yaransa, yan kungiyar Gimbiya Academy da suke taka leda a kasar Norway, a can nahiyar Turai.

Wasu daga cikin yaransa sun bayyana ma majiyar Legit.ng irin amfanin da suke samu daga Coach Sani, inda suka ce yana kara musu kwarin gwiwa, kuma duk girman abokan karawarsu baya tsorata, yak an fada musu “Kafa biyu suke da shi, kuma kafa biyu kuke da shi, duk abinda zasu yi, zaku iya.”

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng