Firaministan Ethiopia ya yi murabus
- Firaministan Ethiopia Hailemariam Desalegn ya yi marabus daga mukaminsa
- Firaminista Hailemariam Desalegn da ya dare kan kujersa tun shekarar 2012
- Firaministan ya ce, gwamnatinsa karkashin jam’iyyar hadaka ta EPRDF za ta sake kafa sabon tarihi ta hanyar mika mulki cikin lumana a kasar
Firai ministan Ethiopia Hailemariam Desalegn ya yi marabus daga mukaminsa bayan wani dadadden rikicin siyasa, matakin da ake kallo a matsayin sabon abu a kasar da ke yankin gabashin Afrika.
Fira minista Hailemariam Desalegn da ya dare kan kujersa tun shekarar 2012, ya yanke shawarar murabus ne bayan watannin da aka dauka ana fama da jerin zanga-zangar adawa da gwamnati da kuma alamomin da suka bayyana na baraka a hadakar jam’iyya mai mulki.
DUBA WANNAN: Hijabi: An karrama Firdausi Amasa a wani babban taro
A jawabinsa da aka watsa ta kafar talabijin, Hailemariam ya ce, ya yi aiki tukuru don magance matsalolin da Habasha ke fama da su, kuma a cewarsa, ya yi amanna, matakin da ya dauka na murabus na cikin magance matsalolin.
Firai ministan ya ce, gwamnatinsa karkashin jam’iyyar hadaka ta EPRDF za ta sake kafa sabon tarihi ta hanyar mika mulki cikin lumana a kasar.
Sai dai Hailemariam zai ci gaba da jagoranci har zuwa lokacin da Majalisar Dokokin kasar da kuma jam’iyyar za su tabbatar da murabus dinsa a hukumance.
Titunan birinin Addis Ababa sun yi tsit bayan sanarwar ba za ta ta murabus din Firaministan.
Duk da cewa, Habasha na daya daga cikin matalautan kasashe a Afrika, Hailemariam ya ci gaba da kokarin inganta tattalin arzikin kasar.
Kawo yanzu babu cikakken bayani game da wanda zai maye gurbinsa.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng