Hukumar Sojin kasa za ta bayar da N3m ga duk wanda ya yi sanadiyar damko Shekau
Hukumar Sojin ƙasa ta Najeriya, ta tanadi tukwicin Naira miliyan uku ga duk wanda ya bayar da sahihin rahoto da zai taimaka wajen damƙo Abubakar Shekau, jagoran ƙungiyar ta'adda ta Boko Haram.
A kwanaki biyu da suka gabata hukumar ta bayyana cewa, Shekau ya arce daga dajin Sambisa, inda yake basaja da shiga irin ta mata sanye da hijabin sa.
Kakakin hukumar sojin na ƙasa, Birgediya Janar Sani Kukasheka Usman, shine ya bayar da wannan sanarwa da cewar, duk wanda ke da ingataccen rahoto to sai ya kira lambar wayar hukumar ta 193.
Janar Usman yake cewa, Shekau yana basaja ne sanye da hijabi mai launin baƙi ko shudi, inda daga wata majiya mai ƙarfi ta tabbatar da Shekau sanye da baƙin hijabi a gani na ƙarshe da aka yi masa.
KARANTA KUMA: Zargin rashawar N10m : Wata kungiya ta bai wa sufeto janar na 'yan sanda wa'adin awanni 48
Ya kirayi sauran mambobin ƙungiyar akan su fito daga maboyar su tare da yin saduda domin yi masu hukunci na jin kai.
A yayin haka kuma, jaridar Legit.ng ta ruwaito cewa, shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya ziyarci mahaifarsa ta garin Daura a ranar Alhamis din da ta gabata, inda ake sa ran zai shafe kwanaki uku kafin ya koma fadar sa ta Villa.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:
https://facebook.com/naijcomhausa
https://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng