Tunatarwa gareka ya shugaba Buhari: Kan alkawarinka a 2015 na yadda zakayi bayan ka gama da Boko Haram

Tunatarwa gareka ya shugaba Buhari: Kan alkawarinka a 2015 na yadda zakayi bayan ka gama da Boko Haram

- A jawabin karbar rantsuwarka, 29 ga watan Mayu, 2015, ka lashi takobin gamawa da kungiyar Boko Haram mai zaluntar jama'a da sunan addini

- Ka ce da an gama yakin gwamnatinka zata duba usulin yadda abi ya faru don magace abkuwar irin hakan a nan gaba

- Fata na kar ka manta har lokacin zabe yazo, ko kayi takara, ko baka yi ba, ko ka ci zabe ko baka ci ba, ka bar baya mai kyau mai dorewa, kan wannan lamari

Wannan rubutu ra'ayin marubuci ne, ba lallai na shafin jaridar Legit.ng ba

Tutatarwa gareka ya shugaba Buhari: Kan alkawarinka a 2015 na bayan ka karar da ta'addancin Boko Haram
Tutatarwa gareka ya shugaba Buhari: Kan alkawarinka a 2015 na bayan ka karar da ta'addancin Boko Haram

Ya shugaba, sanin kowa ne cewa, duk kasashen musulmi babu wacce take harkar Almajirta, na haifar yara rututu qanana, a watsar dasu su nema wa kansu sutura, abinci da rayuwa, basu fahimtar kome na rayuwa banda gararamba a tituna, ga rashin ilimi na zamani, ga rashin gobe mai-kyau, iyayen basu damu ba, mu masu hankali bamu yi komai a kai ba.

READ IT IN ENGLISH HERE/KARANTA WASIKAR DA TURANCI: AN OPEN MEMO TO THE PRESIDENT ON FINDING THE ROOT CAUSES OF BOKO HARAM TERRORISM AFTER ITS DEFEAT

Arewacin kasar nan kaf, babu wanda talakka a zamanin nan ya yarda da hangen nesansa, da siyasarsa, da karfin kalamansa kamar ka ya shugaba. Wannan ita ce babbar dama, tun bayan kwanta-damar su Sardauna, ta ka saita wa yankin nan al'amari, ka 'yanta 'ya'yanka, domin ka ceci jama'armu, ka ceci dukkan jama'ar Najeriya daga sabon ta'addanci da zai zo bayan Boko Haram.

Nayi farin-ciki matuka, da na saurari jawabinka a ranar 29 ga Mayu, a 2015, fiye da ma yadda ka ambaci Atishai a matsayin cewa muma mutane ne a cikin al'ummar Najeriya, da fadinka na cewa, bayan ka gama da kungiyar ta'addanci da ta wargaza wa kasar mu lamari, ta dai-daita al'ummarmu, ta tarwatsa kimarmu a idon duniya, ta kuma farkar damu yadda aka barmu a baya a fannin ilimin zamani, musamman kimiyya, da zumunci ga juna, so da kauna ya kau, zaka kuma bididdigin me ya haifar da lamarin domin magance shi. Sai dai gashi har an kusa shiga zabuka, amma yakin kawai aka iya iyarwa, kar lokaci ya qure.

LABARU MASU ALAKA: Kasashe 25 mafi karfin soji a duniya

Abin ayi kuka, kuma muna yin kukan, cewa cikinmu ne, 'ya'yanmu, da 'yan-uwanmu, farko a jinsinmu na bil-Adama, sannan a nahiyarmu ta bakake, kuma a kasar mu ta Najeriya, a yankinmu na zumuncin jama'ar Arewa, muka tashi muke kashe junanmu, da sunan yankin gabas-ta-tsakiya, wadanda basu ma san muna yi ba, ko kuma basu damu da walwalarmu ba.

Kasar Saudiyya ta aiko da littattafai na zafafa ra'ayi, a 1980s, haka ma kasar Iran, da sunan juyin-juya hali, sun iza mana tsana da kiyayya ga juna, da ma kisan juna da batanci. A gefe daya kuma, mun kasa zama da kiristocin cikinmu lafiya, da marasa addinai, da ma masu addinai na gargajiya.

Mun koma kabilu mabanbanta, mun gina katangun kiyayya daga cakuduwarmu da auratayya, da mutumta juna, da ma kula da kowannenmu tamkar uwarmu daya. Mun zama shirmammu marasa alkibla, mun baiwa wasu lasifiqa suna yayata tsana da kishin akidun banza a kullum, a gari, a tasha, a rediyo, a masallatanmu da cocinanmu, mutumtakarmu ta kau, babu kuma wanda yake iya kwabar wadannan mutane masu 'wa'azi'.

DUBA WANNAN: Budaddiyar wasika zuwa ga Abubakar Shekau

Sai kawai, Boko Haram ta faro, ina aka dauko ta? Ya shugaba, a akidun irin littattafai da tuta da Janar Buratai yake kawo maka daga SAMBISA ake samo Boko Haram, kamar dai ta Maitatsine, almajirai aka koyawa, da sunan jihadi, da sunan kafa tsohuwar daula ta Usmaniyya Fodio, ko kuma ta Bagadaza da Al-Sham.

Wadannan yaran, almajirai, sune dai Boko Haram ta koya wa akida, sune kuma sojojin lokacin Muhammadu Marwa Tatsine, da ma ba'a basu ilimin boko ba, sai suka dauka haramun ce, tunda mun hana su suna yara, yanzu zasu hana mu ta karfi da girmanmu.

Ya shugaba Muhammadu Buhari, ban sani ba ko zaka yi takarar zabe a badi, ban sani ba ko in kayi zaka ci, ban sani ba ko zaka kai shekarun da muke fata muga kyakkyawar niyyarka, amma ka sani, kai ne na karshe, a jerin mazan-jiya, ko dai ka fitar dasu kunya, ka hana almajirci, ko kuma in zamaninmu yazo, mu hana, amma kuma mu ajje a tarihi cewa baku yi mana wannan hobbasa ba, baku kuma aza koda damba ba.

KARANTA: ILIMIN TAURARI a KIMIYYANCE, Wato Cosmology

In ka hana harkar almajirici, kamar ka ceci miliyoyi ne, daga qangin bauta, ka ceci yara da aka hana su gobensu, wadanda kuma ka-iya zagayowa su hana mu da 'ya'yanmu tamu goben, kamar yadda ka saba fadi; jiki-magayi, mun dai ji a Boko Haram, munji a Maitatsine, munji a rikicin addini da dama, a Pulato, a Kano, a Benuwai, a Maiduguri, a Zamfara, a Taraba, kuma ga alama zamu ci gaba da ji, in baka dauki mataki ba.

Fada da bindiga, ko tura bataliyar kwantar da tarzoma a wadannan wurare, shine mataki na farko, amma kashi na biyu, shine; kamar yadda ka fadi, bin diddigin inda aka baro kima da mutumta juna, da son juna da zama lafiya, muka koyo qiyayya da kisa da qeta, don farantawa Larabawa ko Fashawa, ko wasu daga wata kasa rai, ko addinai ko siyasar wani yanki a duniya.

DUBA: KIMIYYA: Asalin Dan-Adam a Kimiyyance

YA shugaba Muhammadu Buhari, in ka sanya dokar tantance wa'azi a mujami'u da masallatai, ka rage yada tsana da kusan rabi. In ka hana almajirta, ka toshe hanyar samarwa jihadin gobe mayaqa, sojoji da 'yan barandan siyasa. In ka bi duk kafar yada tsana ka sanya ido, da hukunci ga masu sayar da kiyayya, da jama'a, da sunan addinai ko aqidu, ka kore rashin tabbas dinmu ta gobe, wadda babu ku a cikinta.

Ya shugaban kasa, kafi kowa sanin yadda kasar nan take kwance a da, Arewa mai dadi da muke karantawa a Magana Jari Ce, da Ruwan Bagaja, da Tatsuniyoyin Da, babu wani ta'addanci, babu wata qyamar Bamaguje ko Majusi, ko Kirista ko Musulmi, kowa kasuwa daya yake zuwa, wurin Alkali daya, wurin Sarki daya a share masa hawaye. Haka na taso ina ji, haka nake so in gani, ba wannan rikitacciyar al'umma ba maras tsari.

In ka sanya dukkan gwamnonin nan da ake almajirta a jiharsu, su fara mika dokoki ga majalisunsu, da kotunansu, da masallatai, da makarantu, da markaz-markaz, da cibiyoyin addinai, da zaurukan shawara, da Islamiyyoyi, da fadojin sarakunan gargajiya, zuwa ga talakawansu, a wata shida za'a iya kawo karshen Almajirta musamman ta kananan yara.

Sai su koma gida, in yaso daga masu shekaru 14 sa iya ci gaba da almajirtar suna sana'a da karatun Boko na yamma bayan na saffe sun tashi, su kuwa saura qananun yaran nan, suyi karatun allo a gida, tare da na Bokon zamani, a gama su je gida, Innarsu ta sanya musu tuwo suci, dare yayi suyi bacci suna jin tatsuniya daga bakinta. Haka aka yi mana muna yara, haka nake so kowanne haifaffe ya samu, ba rayuwar tsumma ba, da wulakantuwa da sunan karatun addini.

Duk uban da ya iya haifa, to dolensa ne ya ciyar, haka Kabilar Igbo keyi da 'ya'yansu, haka kabilar Yarabawa keyi, haka Nupawa keyi, haka Tivi da Igala keyi, haka Bendel keyi, haka Ikwerre keyi, haka Larabawa keyi, haka Iraniyawa keyi, haka Turawa da Yahudawa da Chanawa da Indiyawa keyi, kai hatta Awaki da Birrai da Zakuna da Giwaye da Aladu a daji basu yasar da diyansu suna qananu.

Menene matsalarmu Hausawa da Kanuri da Fulani? In dai jakanta ce tayi mana yawa, to ko dole mu farka muyi maganinta kafin ta hadiye mu. Nakan yi tunani ya Baba, shin wai ni kadai ne nake iya gani da tunanin haka? Masu kudi su shiga gidan mai, da katuwar mota, da 'ya'yansu a AC, su sha, almajirai na kewaye da motar tasu, su gama su fizgi mota su tafi?

Na shekara 12 kenan ina wannan fafutuka ta rubuce-rubuce, mika can, aika can, duk inda na ga taron manya, sai nayi maza na kwaso takarduna na rarraba, na hango Boko Haramun tun kafin ta faru, na rubuta, na aika, na buga, kowanne Gwamna ko Sarki sai dai ya karbi takarda ta yace zasu duba, 'yan majalisun arewa, sarakunan gargajiya, amma shiru, sai kara ma tuttulo yaran nan ake yi birane da robobi cikin tsumma. Sa'ar dai kawai jama'armu sun farga yanzu, kowa yazo wuya kan batun nan.

A shekarun nan kaf, ci-gaban da muka iya samowa yaran nan bai wuce na tsangaya a Kano ba, hana Almajirta a wasu sashen na birane, Kaduna da Kano da Abuja, sai kiraye-kirayen Sarkin Musulmi na a daina almajirta hakan. Da Shugaba Jonathan ya karbi rubutun, wasu daga cikin kuduran takardar kawai ya iya dauka, ya kuma yi hobbasa da rawar gani, madalla.

GA RUBUTUN YADDA ZA'A YI A NAWA HANGEN: The Almajiri System; Resolve of a Right Thinking Nation

Ya shugaba, in ka sanya sabon shiri a kafafen yada baru, na da, da na zamani, na yada zamantakewa, soyayya, da kimanta juna, da auratayya tsakanin kabilu, daga addinai, to ka kore banbancin kabilu baki daya. Misali: duk auren da ya hada wasu kabilu biyu ya sami tagomashi daga gwamnati, in ya haifar da tsatso, ya sami karin kyauta, wannan zai shafe kabilanci da bangaranci tsakanin 'yan Najeriya.

Wannan dai hange ne na masu ganin kamar akwai sabbin hanyoyi na canja akalar Najeriya, fatanmu, ku dattijai ku yi mana jagora. Ba yin titi da kawo wutar lantarki ne kadai aikinku ba a matsayin manyan kasa, ba wai sana'a da tsaro ne kadai aka zabo ku ku kawo ba. Harda alkibla ga al'umma, da samar da kyautayi da mutumtaka wadda aka san mu da ita a da can.

KARANTA: Sarkin Musulmi da shugaban Kirista sun sha alwashin yaye talauci a tsakanin al'umma

Gobenmu zata yi kyau idan kun kafa damba a yau, kafin ku fara kamfe na siyasa, kafin ku manta da Boko Haram kamar yadda kuka manta da Maitatsine, bayan an gama yakin. A koma a tuge tushen ta'addanci, kar wani kma ya dora wasu a kai a gobe.

Nagode dattijon shugaba,

Daga Mubarak Bala Muhammad, (sms +2348032880989) @MubarakBala,

Yardajje daga Kungiyoyin farfado da mutumtaka a fadin Najeriya.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel