Kankamo: Idan na bawa mata ta kudi mutuwa zan yi - Magidanci ya fadawa kotu
- Wani magidanci, Stephanie Enebeli, ya shaidawa wata kotu a jihar Legas cewar zai iya mutuwa idan ya bawa matar sa kudi
- Enebeli na bayyana hakan ne yayin mayar da martani ga bukatar matar sa na neman saki a gaban kotun
- Matar Enebeli, Eunice, ta zarge shi da nuna halin ko-in-kula a kanta da kuma 'ya'yan da suka haifa
Wani magidanci, Stephanie Enebeli, dan shekaru 55 mai sana'ar tela ya shaidawa wata kotu dake zamanta a Igando dake jihar Legas cewar zai iya mutuwa matukar ya bawa matar sa kudi.
Enebeli na bayyana hakan ne a matsayin martani ga bukatar matar sa na neman kotu ta raba aurensu bisa halin ko-in-kula da Enebeli ke nunawa a kanta da 'ya'yan da suka haifa.
"Na daina bawa mai dakina kudi tun bayan da ta gudu daga gidana kuma ta tare da wani mijin. A al'adar garinmu, idan ka bawa matar ka kudi bayan kun rabu ko ta guje ka, to mutum mutuwa zai yi, ni kuma ban shirya mutuwa yanzu ba," a cewar Enebeli.
Enebeli ya kara da cewar "Eunice ta kore ni daga gidan da muke zaune ta karfin tsiya, yanzu haka sai zaman karo nake yi a gidan abokina yayin da ita kuma ke yawon bin maza."
DUBA WANNAN: Miijina ya yi min bugun dawa saboda kawai na fita na kada kuri'a ranar zabe - Wata mata ta sanar da kotu
Eunice, mai shekaru 36 a duniya, ta karyata zargin da mijinta ke yi mata tare da shaidawa kotun cewar Enebeli har barazanar kashe ta ya yi duk da cewar ita ce ta saya masa keken da yake dinki domin ya samu sana'a.
Eunice, uwar 'ya'ya uku, ta roki kotun da ta raba aurensu domin babu amfanin auren tunda ita ke biyan kudin hayar gidan da suke zaune da kuma daukan dawainiyar yaran da suka haifa.
Da yake zartar da hukunci, alkalin kotun, Mista Akin Akinniyi, ya ce kotun bata da wani zabi da ya wuce ta raba auren dake tsakanin Enebeli da Eunice tunda basu da bukatar yin sulhu balle ci gaba da zama tare. An barwa Eunice mallakin yaran da suka haifa.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng