Hadarin mota: Akalla mutane 150 ne suka rasa ransu a jihar Jigawa

Hadarin mota: Akalla mutane 150 ne suka rasa ransu a jihar Jigawa

- Akalla mutane 150 ne suka rasa ransu a jihar Jigawa

- Angus Ibezim shine ya sanar wa da manema labarai hakan

- An fi samun haddurran tare kuma da salwantar rayuka a shekarar 2017 kan 2016

Wani mummunan labarin da ke iske mu daga majiyar mu na bayyana cewa akalla rayuka 150 ne kawo yanzu suka salwanta sannan kuma wasu 556 suka jikkata a sakamakon hadduran ababen hawa 170 da suka auku a jihar Jigawa cikin shekarar da ta gabata ta 2017.

Hadarin mota: Akalla mutane 150 ne suka rasa ransu a jihar Jigawa
Hadarin mota: Akalla mutane 150 ne suka rasa ransu a jihar Jigawa

KU KARANTA: An baiwa sifeto janar na 'yan sandan Najeriya wa'adin kwana 2

Shugaban hukumar nan ta dogarawan hanya mallakin gwamnatin tarayya na shiyyar jihar mai suna Angus Ibezim shine ya sanar wa da manema labarai hakan a yayin firar da yayi da su a ofishin sa dake a garin Dutse, babban birnin jihar.

Legit.ng ta samu haka zalika cewa wasu alkalumman da ya bayar har ila yau sun nuna cewa an fi samun haddurran tare kuma da salwantar rayuka a shekarar 2017 idan aka kwatanta da shekarar 2016.

Haka ma kuma Wani saurayi mai akalla shekaru 27 a duniya mai suna Ifeanyi Ede a yau dinnan Alhamis ya gurfana a gaban alkalin wata kotun Majistare mai daraja ta daya a garin Abuja bisa zargin sa da ake yi na cinnawa gidan budurwar sa wuta.

Dan sanda mai gabatar da kara mai suna Idowu Lawal kamar yadda muka samu tun farko ya bayyanawa kotun cewa shi dai wanda yake tuhumar ya bankawa gidan budurwar sa mai suna Esther Yahaya dake zaune a garin Kubwa, Abuja wuta a ranar 5 ga watan nan da muke ciki.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng