Yaki da rashawa: Jerin wasu tsoffin gwamnoni dake fuskantar tuhume tuhumen satar makudan kudade
Tun a tsakanin shekarar 2003 – 2007, zamanin mulkin tsohon shugaban Cif Olusegun Obasanjo ne aka dinga samun tsofaffin gwamnoni suna aikata wakaci waka tashi da kudaden jihohinsu suna fuskantar shari’a.
Sai dai abin takaicin shi ne har yanzu akwai tsofaffin gwamnonin da an kasa hukuntasu game da ire iren zunubban da suka tafka yayin da suke kan mulki, duk kuwa da namijin kokarin da hukumar yaki da rashawa, EFCC ke yi game da hakan.
KU KARANTA:
Wata kungiyar mai zaman kanta ta wallafa, TransparencIT Nigeria ta wallafa sunayen wasu tsofaffin gwamnoni guda 23 da hukumar EFCCta maka su gaban Kotu bisa tuhume tuhumen satar kudaden jihohinsu a zamanin da suka yi mulki.
Saminu Turaki - N36bn
Murtala Nyako - N29bn
Danjuma Goje - N25bn
Timipre Sylva - N19.2bn
Abdullahi Adamu - N15bn
Attahiru Bafarawa - N15bn
Otunba Alao-Akala - N11.5bn
Ibrahim Shehu Shema - N11bn
Aliyu Akwe Doma - N8bn
Gbenga Daniel - N7bn
Chimaroke Nnamani - N5bn
Babangida Aliyu - N5bn
Rasheed Ladoja - N4.7bn
Orji Uzor Kalu - N3.2bn
Gabriel Suswan - N3.1bn
Ahmadu Umaru Fintiri - N2.9bn
Jolly Nyame - N1.64bn
Sule Lamido - N1.3bn
Joshua Dariye - N1.16bn
Ahmed Sani Yerima - N1bn
Ikedi Ohakim - N270m
James Bala Ngilari - N167m
Sai kuma shugaban majalisar dattawa, Sanata Bukola Saraki da ake tuhumarsa da kin bayyana gaskiyar adadin kadarorinsa da darajarsu.
Si dai Legit.ng ta ruwaito yan Najeriya da dama basa jin dadin irin tafiyar hawainiyar da shari'un wadannan tsoffin gwamnoni ke yi, musamman idan aka kwatanta da kanana barayi, wanda ana kama su sai gidan Yari.
Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
ko a http://twitter.com/naijcomhausa
KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng