Nagari, Nakowa, Buhari kenan – Inji wani gwamna daga jam’iyyar PDP

Nagari, Nakowa, Buhari kenan – Inji wani gwamna daga jam’iyyar PDP

A yayin da zabukan 2019 ke kara karatowa, ana cigaba da samun bambamcen ra’ayoyi game da yiwuwar tsayawa takarar shugaban kasa Muhammadu Buhari, ko kuma akasin haka.

A baya Legit.ng ta kawo maku rahoton wata doguwar wasika da tsohon shugaban kasa Cif Olusegun Obasanjo ya aika ma shugaban kasa Muhamamdu Buhari, inda ya gargade shi game da sake tsayawa takara, a cikin ya shawarci Buhari kada ya kuskura ya tsaya takara a 2019.

KU KARANTA: An bankado musabbabin da yasa ake kashe yan Najeriya a kasar Afirka ta kudu

Ba’a gama tattauna wannan wasika ba, kwatsam sai shi ma tsohon shugaban kasa, Janar Ibrahim Babangida ya bi sawun Obasanjo, inda ya yi kira ga Buhari da kada ya sake tsayawa takara.

Nagari, Nakowa, Buhari kenan – Inji wani gwamna daga jam’iyyar PDP
Buhari Tinubu da Gwamnoni

IBB kamar yadda aka fi saninsa, ya bayyana matsayarsa ne ta bakin Kaakakinsa, Akeem Afegbua, inda yace Buhari ya gaza tabbatar da tsaro a Najeriya, don haka ya koma gida ya huta.

Abinka da siyasa, mai baiwa koya yancin tofa albarkacin bakinsa, sai aka jiyo gwamnan jihar Akwa Ibom, kuma jigo a jam’iyyar PDP, Emmanuel Udom yana bayyana nasa ra’ayin, inda a nasa hasashen, Buhari ya ci zabe ya gama a 2019.

Gwamna Udom yace dalilinsa na fadin haka kuwa bai wuce yadda Buhari ke rungumar kowa da kowa ba tare da la’akari da bambamcin jam’iyya ba, musamman a tsakanin gwamnonin Najeriya.

“SHugaban kasa Buhari zai lashe zabe a karo na biyu idan har ya yanke shawarar tsayawa takara, saboda baya fifita gwamnonin APC akanmu ina yi masa lakabi da Nagari, nakowa.” Inji shi.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng