An daga zaman majalisar dattijai na yau saboda lalacewar na'urorin sanyaya daki
- A yau ne majalisar dattijai ta dage zamanta zuwa ranar Talata ta satin gobe saboda na'urorin sanyaya zauren majalisar sun samu tangarda
- Shugaban majalisar, Bukola Saraki, ya umarci daga zaman majalisar domin a samu damar gyaran na'urorin
- Rahotanni na alakanta daga zaman majalisar da tashin gobara a wani bangare na ginin majalisar
Majalisar dattijai ta daga zamanta na yau zuwa ranar Talata ta satin gobe saboda na'urorin sanyaya zauren majalisar sun samu tangarda.
Mamba a majalisar, Sanata Abdullahi Gobir, ya gabatar da kudirin daga zaman majalisar bisa hujjar cewar babu dadin zama a zauren majalisar saboda rashin aikin na'urorin sanyaya daki.
Shugaban majalisar, Bukola Saraki, ya amince da wannan kudiri na Sanata Gobir tare da yin umarnin a gyara na'urorin yayin hutun karshen satin nan da zamu shiga.
DUBA WANNAN: Ba na nadamar rabon kaskon suya ga 'yan mazaba ta - Sanatan Najeriya
A wani labarin mai alaka da wannan, Legit.ng ta sanar da ku cewar wani sashe na ginin majalisar tarayya ya kama da wuta da safiyar yau.
Wasu rahotanni sun bayyana cewar daga zaman majalisar nada nasaba da tashin wutar da ake zargin ta fara ne daga dakin ajiyar na'urorin sanyaya zauren majalisar.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng