Ganduje ba zai iya ba mu wajen kiwo ba - Fulani makiyaya

Ganduje ba zai iya ba mu wajen kiwo ba - Fulani makiyaya

- Fulani makiyaya da ke jihar Kano sun ce wurin kiwon da ake da shi a jihar bai wadaci shanun su ba balantana bamakwabta su

- Gwamnatin Ganduje ta ce duka makiyayan kasar su dawo jihar Kano su cigaba da kiwon dabobin su

Fulani makiyaya a Najeriya sun ce basu da tabbaci akan alwashin samar da wurin kiwo ga Fulanin da ke kasar baki daya da da gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya yi musu.

Wasu makiyaya da ke jihar dai sun ce wurin kiwon da ake da shi bai wadaci shanun cikin jihar ba, ballantana a bude kofa ga makwabta su.

A cikin kwanakin baya gwamnatin Kanon ta yi wa Fulanin makiyayan Najeriya wannan tayin, wanda take ganin cewa zai taimaka wajen kawo karshen rikcin makiyaya da manoma da ya addabi wasu sassan kasar.

Ganduje ba zai iya ba mu wajen kiwo ba - Fulani makiyaya
Ganduje ba zai iya ba mu wajen kiwo ba - Fulani makiyaya

Amma duk da haka wasu makiyaya a jihar na cewa suna maraba da tayin da gwamnatin Ganduje ta yiwa 'yan uwansu na samar musu wurin kiwo, matakin da suke cewa zai cire musu dangi daga halin kaka-nika-yin da suka tsinci kansu.

KU KARANTA :

Sai dai da yawa daga cikin Fulanin na kokwanto dangane da faruwar lamarin, idan suka yi la'akari da cewa shanunsu da ke gida ma wata rayuwa suke yi ta hannu-baka-hannu-kwarya, sakamakon zargin da suke na warwason da mahukunta ke yi da ragowar buratali da wuraren kiwon da ke jihar.

Sai dai duk da irin wannan kyakyawan kudirin da Kano ke ikirarin kudurtawa, makiyayan sun ce da wuya su samu cikakkiyar gamsuwa, sai sun gani a kasa.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng