Mataimakan darektoci 150 sun fadi wan-war a jarrabawar karin girma

Mataimakan darektoci 150 sun fadi wan-war a jarrabawar karin girma

- A kalla mutane 150 masu rike da mukamin darekta a gwamnatin tarayya sun fadi jarrabawar karin girma

- Shugabar hukumar kula da ma'aikatan gwamnatin tarayya, uwargida Winifred Oyo-Ita, ta sanar da haka a jiya yayin wani taro

- Mutane 290 masu rike da mukamin mataimakin darekta ne suka zauna jarrabawar

Shugabar ma'aikatan gwamnatin tarayya, Winifred Oyo-Ita, ta ce mutane 140 ne daga cikin masu rike da mukamin mataimakin darekta 190 suka iya yin nasara a jarrabawar karin girma da suka rubuta.

Oyo-Ita ta bayyana haka ne a jiya yayin halartar wani taro a Abuja.

Mataimakan darektoci 150 sun fadi wan-war a jarrabawar karin girma
Winifred Oyo-Ita

"Ina mai farincikin sanar da ku cewar yanzu mun warware matsalar karin girma ya zuwa mukamin darekta a aikin gwamnatin tarayya," Oyo-Ita ta fadawa mahalarta taron.

DUBA WANNAN: Kotu ta kwace fasfo din tsohuwar minista da ake tuhuma da badakalar wawure miliyan N450m

"Fiye da mutane 190 masu rike da mukamin mataimakin darekta ne suka zauna jarrabawar neman zama darektoci a gwamnatin tarayya amma mutane 140 ne kawai suka yi nasara. Hakan na nufin cewar mutane 150 sun fadi wan-war a jarrabawar," a cewar Oyo-Ita.

Oyo-Ita ta jinjinawa hadin kai da goyon baya da shugaba Buhari ke bayarwa wajen warware matsalolin aikin gwamnatin tarayya.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng