Kudin ajiyar Najeriya na kasashen waje ya karu da dala bliyan $42.8bn

Kudin ajiyar Najeriya na kasashen waje ya karu da dala bliyan $42.8bn

- Kudin ajiyar Najeriya na kasashen waje ya karu da dala bliyan $42.8bn

- Dokar hana shigo da kayan abinci da gwamnatin tarayya ta zartar ya sa kudin asusun ajiyar kasashen waje suka karu

Kudin ajiyar Najeriya na kasashen waje ya karu da dala bliyan $42.8bn.

Wasu bayyanai da suka fito daga bakin wani jami’in babban bankin Najeriya, Mista Isaac Okoroafor, ya nuna cewa kudaden dake asusun ajiya na kasashen wajen na kasa sun karu da dala biliyan $42.8bn.

Isaac Okoroafor,ya bayyana haka ne taron da babban bankin Najeriya ta yi da kungiyar manoman shinkafa (RIFCAN) a safiyan yau a Abuja.

Kudin ajiyar Najeriya na kasashen waje ya karu da dala bliyan $42.8bn
Kudin ajiyar Najeriya na kasashen waje ya karu da dala bliyan $42.8bn

Ya ce dokar hana shigo da kayan abinci daga kasashen waje da gwamnatin tarayya ta zartar musamman shinkafan da ake noma a kasar yasa kudin dake cikin asusun kasashen waje ya karu.

KU KARANTA : Rikicin Benue: Majalissar Dattawa ta fara yiwa Gwamna Samuel Ortom bincike akan kashe-kashen da ake zargin makiyaya sunyi a jihar sa

Noman shinkafa yana daga cikin shirin Anchor Borrowers da gwamnatin tarayya ke amfani da shi wajen bunkasa asusun ajiya kasashen waje na Najeriya.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku ci gaba da bin mu a

Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa

Da Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng