Karanta wasu gyaran fuska guda 8 masu muhimmanci da yan majalisa suka yi ma dokokin zaɓe
Rana bata karya, sai dai uwar diya ta ji kunya, inji Hausawa, wannan shi ne kwatankwacin lamarin da ya faru jiya Laraba, 14 ga watan Feburairu, a babban birnin tarayya Abuja.
Legit.ng ta ruwaito majalisun dokokin Najeriya da suka hada da yan majalisar wakilai su 360, da kuma yan majalisar dattawa su 109 sun amince da garambawul ga dokokin hukumar zabe don inganta zabukan da hukumar INEC za ta dinga shiryawa.
KU KARANTA: Alhamdulillah: Allah ya ceto rayuwar wani jigon jam’iyyar PDP daga hannun masu garkuwa da mutane
Mun kawo muku gyaran fuska guda 8 daga cikinsu:
1- AIKA SAKAMAKON ZABE: Majalisa ta baiwa hukumar zabe mai zaman kanta, INEC, ikon tattara sakamakon zabe da aikasu daga rumfunan zabe zuwa shelkwatar hukumar don tabbatar da sahihanci zaben da kauce ma aringizo.
2- WALLAFA RAJISTAN MASU ZABE A YANAR GIZO: Daga yanzu hukumar INEC za ta dinga wallafa sunayen masu zabe da suka yi rajista, kwanaki 30 kafin ranar zabe, don kauce ma sauya rajistan masu zabe a ranar zabe.
3- TANTANCE MASU KADA KURI’A: An baiwa INEC daman bin watan hanyar da ta dace don tantance masu kada kuri’a a ranar zabe, hatta ta amfani da kimiyya da fasaha.
4- HANA YIN DAUKI DAURA: Sabon gyaran fuskar da aka yi ma dokokin zabe sun hana jam’iyyun siyasa aikata dauki daura game da yan takarkarunsu ta hanyar fitar da wasu ka’idoji da ka iya baiwa wasu shafaffu da mai kadai daman yin takara.
5- HANYOYIN MAGANCE RIKICI: Garambawul din da aka yi ya samar da ingantattun hanyoyin fitar da dan takara daga cikin jam’iyyu, tare da samar da hanyoyin magance duk wata fitina da ka iya tasowa bayan hakan.
6- KUDADEN TAKARA: Dokar ta kayyade iya kudin da ake tsammanin dan takara zai iya kashewa a yayin yakin neman zabensa, da kuma kayyade kudin siyan takardar bukatar tsayawa takara daga wajen jam’iyya.
7- SAUYA DAN TAKARA: Dokar ta bukaci a mika sunayen yan takara akalla kwanaki 90 kafin ranar zabe, inda kuma ta tanadar da kwanaki 30 kafin zabe don mika sunan wani sabon dan takara idan har an canza na farko, haka zalika duk wanda a karan kansa ya janye takararsa sai ya sanar da INEC.
8- MUTUWA: Idan kuma mutuwa ta yi halinta ga wani dan takara kafin ranar zabe, Dokar ta bukaci a dakatar da zaben har na tsawon kwanaki 21, don baiwa jam’iyyu kwanaki 14 su sauya dan takara, kwanaki 7 kumayakin neman zabe.
Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
ko a http://twitter.com/naijcomhausa
KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng