Ni ban ce maciji ya haɗiɗiye N36m ba - Inji ma'aikaciyar JAMB
Wata sabuwar ruwaya ta bayyana dangane da rahoton maciji da ya haɗiɗiye N36m a ofishin JAMB reshen jihar Benuwe, inda karamar ma'aikaciya Philomena Chiesche ta bayyana cewa, ma'aikatar ta ƙago labarin macijin ne domin rufe gaskiyar lamarin yadda aka yi sama da fadi da kudaden.
A yayin ganawa da manema labarai na Cable News Network (CNN), Philomena ta bayyana cewa ko sau guda ba bu wanda ya titsiye ta dangane da batun kudaden, kuma ita bata taba cewa maciji ne ya haɗiɗiye su ba.
A cewar wannan ma'aikaciya, ma'aikatar ta JAMB ta ƙago labarin maciji ne da cewar ya sakuda ofishin ajiyar kudi kuma ya haɗiɗiye su a reshen ta na birnin Makurdi.
A baya dai, kakakin ma'aikatar ta JAMB, Fabian Benjamin, ya bayar da rahoton zamba da almundahana a ofishin su dake jihar Benuwe, wanda hakan ya yi sanadiyar dakatar da sayar da katuka ga dalibai masu buƙatar shiga jami'a domin magance rashawar dake gudana.
Rahoton da ya bayyana a baya shine, Philomena ta shaidawa shugaban na JAMB da tawagar sa cewa, ta gaza gano inda N36m suka shiga na ma'aikatar tun na shekarun baya kafin a daina sayar da katuka ga dalibai.
Inda Philomena ta zauna kan kujerar naƙi da cewar ko sisi bata dauka a cikin wannan kudade ba, sai dai ta bayyana cewa hadimar gidanta ce ta ƙulla tuggu da wani ma'aikacin na JAMB, Joan Asen, inda suka yi tsubbu wajen turo maciji kuma yayi awon gaba da wannan kudade.
KARANTA KUMA: Rikicin makiyaya da manoma: Gwamnatin tarayya ta aika da ma'aikatan NSCDC 1600 don kare garkunan shanu
Legit.ng ta fahimci cewa, akwai rahotanni da suke cin karo da juna dangane da yadda aka nemi kudaden kuma aka rasa, wanda wannan rahoto ya shahara da batutuwansa ke ta gudana a bukunan 'yan Najeriya tare da dandalai na sada zumunta cikin 'yan kwanakin da suka gabata.
A yayin haka ne, hukumar EFCC ta bayyana a shafin ta na sada zumuntar twitter da cewa, ba za ta rangwantawa wannan maciji ba, da ya haɗiɗiye zunzurutun kudi na N36m a ofishin JAMB reshen birnin Makurdi na jihar Benuwe.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:
https://facebook.com/naijcomhausa
https://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng