Kotu ta bada belin matan da ta tsoma hannun dan kishiyar ta a tafasasshen ruwa

Kotu ta bada belin matan da ta tsoma hannun dan kishiyar ta a tafasasshen ruwa

Rahotanni sun kawo cewa wata kotu dake yankin Kuje naa babban birnin tarayya Abuja ta bayar da belin wata mata da aka kira da suna Khadiya Yahaya, bayan kamata da laifin tsomawa dan kishiyarta hannu a cikin tafasasshen ruwa.

Hukumar NAPTIP ne ta maka Khadija Yahaya a kotu dake Bwari Abuja sakamakon kona hannun dan kishiyar ta da ta yi da tafasasshen ruwan zafi.

Hukumar ta sanar da cewa Khadija wacce ke auran wani Mallam Yahaya a matsayin matar sa ta biyu ta aikata haka ne a ranar 12 ga watan Disambar 2017 a gidan su dake hanyar Old block Industry kusa da cocin ECWA a unguwan Chukuku dake yankin Kuje, Abuja.

Kotu ta bada belin matan da ta tsoma hannun dan kishiyar ta a tafasasshen ruwa
Kotu ta bada belin matan da ta tsoma hannun dan kishiyar ta a tafasasshen ruwa

"A wannan rana ne Khadija mai shekaru 30 ta zuba wani sinadarin dake yi wa fatar jikin mutum illa a cikin tafasashen ruwa sannan ta tsoma hannayen dan kishiyar ta mai suna Abubakar Yahaya mai shekaru 2 a cikin wannan ruwa.”

Ko da yake Khadija ta musanta aikata haka alkalin kotun A.O Musa ya bada belinta kan Naira 500,000 tare da takardar shaida daya sannan ya daga sauraron karan zuwa ranar 20 ga watan Fabrairu.

KU KARANTA KUMA: Bance a zabtare albashin yan majalisa ba – Sarki Sanusi

Idan zaku tuna a baya Legit.ng ta rahoto cewa wata mata da aka ambata da suna Khadija Adam tayi wa dan kishiyarta mai shekara daya da watanni shida a duniya lahani.

Tayi ma dan kishiyar nata illa ne ta hanyar tsoma masa hannunsa a cikin ruwan zaki abode ya cinye mata abinci.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng