Da duminsa: Hukumar tsaro ta DSS ta gayyaci Labaran Maku
- A yau ne ofishin hukumar tsaro ta DSS a jihar Nasarawa ta gayyaci tsohon ministan yada labarai, Mista Labaran Maku
- Hukumar DSS ba ta bayyana dalilin gayyatar Maku ba
- Maku ya bayyana cewar ba gaskiya ba ne cewar hukuma ta gayyace shine domin ta tsare shi kamar yadda wasu ke yadawa a dandalin sada zumunta
Ofishin hukumar tsaron farin kaya (DSS) ta gayyaci tsohon ministan yada labarai, Labaran Maku, a yau Laraba.
Hukumar ba ta bayyana dalilin gayyatar Maku ba. Saidai, Maku, ya yi watsi da jita-jitar da wasu ke yadawa a dandalin sada zumunta cewar hukumar zata tsare shi tare da yin kira ga 'yan siyasar Najeriya da su guji yin kalamai da ka iya jawo zubar da jini tsakanin al'umma gabanin karatowar kakar zabe ta 2019.
Maku, tsohon dan takarar gwamnan jihar Nasarawa a zaben 2015 karkashin jam'iyyar APGA, ya yi kira ga 'yan siyasar kasar nan da su saka kishin kasa fiye da banbancin jam'iyya ko bukatar kansu domin kawo cigaba ga jama'a.
DUBA WANNAN: Hadin kan Najeriya iko ne na ALLAH - Buhari
"Na rike mukamin kwamishina a jihar Nasarawa kafin na zama mataimakin gwamna sannan daga baya na zama minista, amma a yau ina yawo na ba tare da tsangwama ba, duk da kasancewar bana rike da kowanne irin mukamin siyasa," inji Maku.
Daga karshe ya yi kira ga gwamnatocin tarayya da jihohi da su dauki matakan kawo karshen rikicin makiyaya da manoma dake ci gaba da lashe rayukan jama'a.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng