An karrama yara 'yan Najeriya mahaddata Al'qur'ani a kasar Saudiyya

An karrama yara 'yan Najeriya mahaddata Al'qur'ani a kasar Saudiyya

- An karrama wasu yara mahaddatan Alqur'ani 'yan Najeriya a kasar Saudiyya

- Yaran sun fito daga makarantar NURUT TILAWAH dake Zaria

- Sheikh Dr. Abdallah Ali Basfar yayi farin ciki da kokarin da makarantar ta ke yi

An karrama yara 'yan Najeriya mahaddata Al'qur'ani a kasar Saudiyya
An karrama yara 'yan Najeriya mahaddata Al'qur'ani a kasar Saudiyya

Cibiyar kula da Haddan Alqur'ani mai girma ta duniya da ke kasar Saudiyya, karkashin jagorancin Sheikh Dr. Abdallah Ali Basfar, ta karrama dalibai mahaddata Alqur'ani daga Najeriya.

Daliban wa 'yanda suka fito daga makarantar NURUT TILAWAH dake garin Zaria, dake Jihar Kaduna, sun isa kasar Saudiyya ne don ziyarar karo ilimi da aikin umara karkashin jagorancin shugaban makarantar Sheikh Nuruddeen Umar Tahir.

DUBA WANNAN: Yadda aka kashe General Murtala Muhammad

A jawabinsa shugaban makarantar ya ce sun fito da tsarin yin haddan Alqur'ani a shekara daya ne don bawa matasa damar haddace Alqur'ani tun kafin suyi zurfi a karatun zamani ta yadda Alqur'anin zai zame musu mabudi, kamar yadda makarantar ta fitar da mahaddata sama da 350 tun kafuwarta.

A maida jawabinsa Sheikh Dr. Abdallah Ali Basfar, yayi farin ciki matuka da irin wannan namijin kokari da wannan makaranta take yi wajen karantar da al'umma littafin Allah, ya kuma yaba da irin cigaban da aka samu tun daga lokacin da ya ziyarci makarantar a shekarar 2005.

A karshe ya saurari karatu daga daliban inda yasa musu albarka.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng