Dole mu kau da kabilanci idan muna son dorewar Najeriya – Dakta Imam

Dole mu kau da kabilanci idan muna son dorewar Najeriya – Dakta Imam

- Dakta Imam ya ce kalubalen da Najeriya ke fusakanta bai rasa nasaba da sace dukiyoyin al'umma ba da cin hanci da rashawa

- Imam ya dole sai mun kawar da kabilanci da nuna babamcin addini kafin mu samu zaman lafiya da hadin kai a Najeriya

Dakta Mohammed Ibn Imam na kwalejin horar da Malamai ta kasa dake Kontogara jihar Neja, yace rashin kishi da mayar da tsarin kasar nan baya a matsayin jigon abinda ya janyo mana halin da muke ciki yanzu.

Yace ya zama dole duk wani mai kishi da son ci gaban kasar ya lalubo hanyar da za a samu hadin kai da zaman tare ba tare da nuna bambamcin addini da kabilanci ba muddin ana son ci gaban tattalin arzikin Najeriya.

Dakta Imam ya bayyana haka ne a wata lacca da ya gabatar a babban taron Murya talaka ta kasa karo na biyu da aka gudanar a Kontogora a ranar ranar Juma’a 9 zuwa 10 ga watan Fabrairu, taronta na biyukenan tun bayan kafa kungiyar a shekarar 2003.

Dole mu kau da kabilanci idan muna son dorewar Najeriya – Dakta Imam
Dole mu kau da kabilanci idan muna son dorewar Najeriya – Dakta Imam

Dakta Muhammad Ibn Imam, wanda ya wakilci Farfaesa Ibrahim A. Gambari, tsohon wakilin Nejariya a majalisar dinkin duniya, yace kalubalen da ke fuskantar kasar, bai rasa nasaba da sace dukiyan al'umma ba, cin hanci da rahsawa, tabarbarewar tattalin arziki, rashin ingancin hukumomi da rashin daidaito.

KU KARANTA : Rikicin Beuwe : Dakarun sojojin Najeriya sun fara gudanar da atisayen gudun muzuru a yankin Arewa na tsakiya

Imam yace kundin tsarin mulkin kasar na bukatar gyaran fuska.

Taron kungiyar Muryar Talaka na kasa karo na bakwai kenan da aka gudanar karkashin jagorancin, Malam Zaidu Bala Kofar Sabuwa, Birnin Kebbi.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng