Hukumar ‘yansanda ta tsare wasu jami’an ta akan laifin yiwa wata shugaban makaranta Frimare dukan tsiya a jihar Ogun

Hukumar ‘yansanda ta tsare wasu jami’an ta akan laifin yiwa wata shugaban makaranta Frimare dukan tsiya a jihar Ogun

- 'Yansandan da suke yiwa shugaban makarantar Frimare sun shiga hannu

- Matar da 'yansada suke yiwa duka tsiya ta bukaci hukumar ta gurfanar da su

Rundunar ‘yansandar jihar Ogun ta kama jami’an ‘yansandan da suke yiwa wata shugaban makarantar frimaren Top Tez Ifo mai suna Ayodeji Orojo, dukan tsiya.

Kwamishinan ‘yansandan jihar Ogun, Ahmad Iliyasu, ya fadawa manema labaru a ranar Talata cewa an tsare ‘yansandan da suka yiwa, Ayodeji Oroji, dukan tsiya kuma za a gurfanar da su da zarar an kammala yi musu bincike.

Legit.ng ta samu rahoton cewa, an samu na’uran stabiliza malakar ofishin ‘yansadar unguwar Ojodu Abiodun dake jihar Ogun da barayi suka sace gidan su wani dalibin makarantar Frimare, David, mai shekaru goma.

Rahoton ya nuna ‘yansanda shida sun kai wa makaranta sammame yayin da dalibai ke karatu.

Hukumar ‘yansandan jihar Ogun ta tsare jami’an 'yansandan da suka yiwa shugaban makaranta Frimare dukan tsiya
Hukumar ‘yansandan jihar Ogun ta tsare jami’an 'yansandan da suka yiwa shugaban makaranta Frimare dukan tsiya

Rahoton ya nuna ‘yansanda shida sun kai wa makaranta sammame yayin da dalibai ke karatu.

Da shugaban makarantar, Ojoro ta tambaye su mai ke faruwa, sai suka yi mata dukan tsiya tare da kwace mata waya a lokacin da take kokarin yin bidiyon dukan da suke mata.

KU KARANTA : Rikicin makiyaya: Kungiyoyin arewa sun bukaci Buhari ya sauke gwamnonin jahohin yankin 4

‘Rahoton ya nuna ‘yansanda sun sako David bayan mahaifiyar sa ta biya N19,000 kudin beli.

Mai magana da yawun rundunar ‘yansadan jihar Ogun, Abimbola Oyeyemi, ya ce rundunar su basu san wanda ake zargi da satan stabiliza karamin yaro bane, Amma DPO ya nemi gafarar hukumar makarantar kuma an warware matsalar.

Orojo ta bukaci hukumar ‘yansanda jihar Ogun ta gurfanar da jami’an 'yansandan da suka ci zarafin ta.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku ci gaba da bin mu a

Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa

Da Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng