An hallaka makiyaya 12, an nemi 14 an rasa a jihar Oyo
Akalla makiyaya 12 sun rasa rayukansu kuma an nemi 14 an rasa a jihar Oyo sanadiyar harin da wasu manoma suka kai musu a karamar hukumar Iseyin na jihar Oyo.
Shugaban kungiyar makiyayan Miyetti Allah, shiyar jihar Oyo, Yakub Bello, wanda ya bayyana wannan abu jiya Talata, 13 ga watan Fabrairu ya ce sun samu wannan adadin ne sanadiyar kuka da iyalan wadanda aka kashe suka kawo sakatariyan MACBAN.
“Yanzu haka, mutane 12 sun tafi da yan sanda kauyen domin daukan gawawwakin. Ba da dadewa ba kuma, wasu mutane 14 sun kawo karan cewa sun nemi mazajensu 14 sun rasa.
Muna sauraron dawowan yan sandan su yi mana bayani kan mutane 14 na kauyen Abu Gaga.”
KU KARANTA: Muna da isashshen sarari ga duk masu son dawowa jam'iyyar mu - PDP
Ya kara da cewa an kashe dabbobinsu da yawa kuma hankalin Fulani ya tashi a garin Iseyin yanzu amma kungiyar samu daman kwantar musu da hankali kuma kada suyi ramuwar gayya.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng