Majalisa ba zauren zarge-zarge bane, Saraki ga Marafa
- Shugaban majalisar dattawa, Dr Bukola Saraki, ya shawarci sanatoci das u daina amfani da majalisar dattawan Najeriya wajen sasanta al’amuran siyasa
- Saraki ya bayyyana hakan a lokacin da Sanata Kabiru Marafa (Zamfara, APC) ya tada wani korafi
- A yanzu haka Marafa da gwamnan jiharsa, Abdulaziz Yari na rigima
A ranar Talata, 13 ga watan Fabrairu, Shugaban majalisar dattawa, Dr Bukola Saraki, ya bayyana cewa ya zama dole a daina amfani da zauren majalisa wajen zarge-zarge da kuma magance wasu rikici da suka shafi wasu ba.
Ya bayyyana hakan a lokacin da Sanata Kabiru Marafa (Zamfara, APC) ya tada wani korafi.
Marafa yayi kokarin zargin wani hadimin gamnan jiharsa, Abdulaziz Yari da zamowa sanadiyan afkuwar wasu rigingimu da dama a jihar.
Bayan sanata Marafa ya kammala koro bayanin al’amarin a takaice, sai Saraki ya umurci Kwamitin da Sanata Ahmed Lawal ke jagoranta kan tsaro da su duba al’amarin da sanatan Zamfaran ya gabatar.
KU KARANTA KUMA: Idan ba a sakewa Najeriya zani ba, za ta watse inji Manyan Kudu
A baya Legit.ng ta rahoto cewa manya daga Yankin Kudancin kasar nan sun zauna a Garin Yenogoa a Jihar Bayelsa inda su ka tattauna game da tsarin Najeriya musamman a karkashin mulkin Shugaban kasa Muhammadu Buhari inda su ka nemi Shugaban ya sauko daga ra'ayin sa.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng