Biki Bidiri: Diyar Osinbajo zata auri dan wata Hajiya, hamshakiyar mai kudi
- Diyar Osinbajo zata auri dan wata Hajiya, hamshakiyar mai kudi
- Mun samu labarin cewa shima hamshakin mai kudi ne da ke da kamfunna
- Za'a yi shagulgulan bukukuwan ne a ranakun Alhamis, 15 da kuma 17, ranar Asabar ga watan Maris
Mun samu daga majiyoyin mu cewa diyar mataimakin shugaban kasar Najeriya Farfesa Yemi Osinbajo mai suna Kiki ta shirya kawo karshen soyayyar da suka dade suna tafkawa da dan wata Hajiya, hamshakiyar mai kudi watau Hajiya Bola Shagaya ta hanyar aure shi.
KU KARANTA: An yi musayar wuta tsakanin yan sanda da makiyaya
Kamar dai yadda muka samu, sunan dan hamshakiyar mai kudin, Hajiya Bola Shagaya, Seun Shagaya wanda kuma muka samu labarin cewa shima hamshakin mai kudi ne da ke da kamfunna masu tarin yawa a ciki da kuma wajen kasar nan.
Legit.ng dai ta samu haka zalika cewa za'a yi shagulgulan bukukuwan ne a ranakun Alhamis, 15 da kuma 17, ranar Asabar ga watan Maris amma kawo yanzu ba'a san inda za'ayi bikin ba.
A wani labarin kuma, Kawo yanzu dai mun samu daga majiyoyin mu cewa akalla shugabannin kasashe biyar ne suka tabbatar da sha'awar su ta zuwa bikin diyar shahararren mai kudin nan na Nahiyar Afrika watau Fatima Aliko Dangote.
Haka nan ma dai mun samu cewa shi ma dai mai kudin nan na duniya kuma mai kamfanin kera kwamfutocin nan watau Bill Gate shima ya sanar da zuwan na sa.
Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da
Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa
KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng