Mugun Likita: Yan sandan Najeriya sun kama gaggan barayi 5 da babban likita ke shugabanta
Jami'an 'yan sandan Najeriya reshen garin Abuja sun sanar da samun nasarar cafke wasu gaggan barayi na mutum 5 da kuma ake zargin wani babban likita ne ke shugabantar su mai suna Dakta Ola Jimade.
Majiyar mu dai ta tabbatar mana da cewa akalla kawo yanzu dukkan mutanen dake zargi da satar sun shiga hannun 'yan sandan sai dai shi shugaban na su ne har yanzu ba'a kama shi ba.
KU KARANTA: Mutane 31 da suka jefa matar Jonathan cikin tsaka mai wuya
Legit.ng ta samu cewa kwamishinan 'yan sandan garin Abuja din mai suna Sadiq Bello ya bayyana cewa wasu masu kishin kasa ne suka kwarmata masu gaggan barayin wanda kuma hakan ya taimakawa su wajen kai samame kafin daga bisani su kama su a maboyar su.
A wani labarin kuma, Wasu gamayyar kungiyoyin arewacin kasar nan sun bukaci gwamnatin tarayya karkashin jagorancin shugaba Muhammadu Buhari da ta saka dokar ta-baci a akalla jihohi hudu daga cikin sha tarar yankin domin tabbatar da tsaro lafiya da kuma dukiyoyin al'umma.
Su dai gamayyar kungiyoyin sun bukaci gwamnatin tarayyar da ta tsayar da dukkan hukumomin tsaro da na siyasar jahohin sannan ta kuma nada shugabannin wucin gadi da za su kawo karshen kashe-kashen da ake fama da shi a jahohin.
Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da
Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa
KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng