Wasu muhimman bayanai guda 7 dake tsakanin Fatima Ganduje da saurayinta, Abolaji

Wasu muhimman bayanai guda 7 dake tsakanin Fatima Ganduje da saurayinta, Abolaji

Sau dayawa, soyayya ne kan gaba cikin alakoki dake hada kan jama’a, ba tare da duba da addini, kabila, yare ko jinsi ba. Tamkar hake ne ya faru a tsakanin Fatima Ganduje da saurayinta Abolaji.

Idan za’a tuna, a watan daya gabata ne Legit.ng ta kawo muku rahoton shirin bikin auren diyar gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje da yaron gwamnan jihar Ogun, Ibikunle Amosun.

KU KARANTA: Ina tsoron fushin ubangiji – Inji wani babban Fasto da ke neman yan mata da Mata mabiyansa

A watan Nuwambar data gabata ne iyayen saurayi Abolaji suka kai gaisuwa ga iyalan Ganduje, tare da ziyarar na gani, ina so, wanda ya samu halartar gwamnoni guda 11 da kuma wasu manyan mutane.

Wasu muhimman bayanai guda 7 dake tsakanin Fatima Ganduje da saurayinta, Abolaji
Masoyan

Daily Trust ta kawo wasu muhimman abubuwa game da masoyan biyu:

- Fatima ta karanci alakar kasashen duniya a jami’ar Amurka dake Najeriya, inda ta kammala da digiri mai daraja na daya.

- Fatima yar gwagwarmaya ce mai kare hakkin bil adama, wanda har ta kai ga ta samar da wata gidauniya mai suna ‘Mu tattauna zamantakewa’, wanda ya mayar da hankali wajen kulawa da ilimin kananan yara da masu bukata ta musamman.

- Shekarun Fatim 23, amma ta jagoranci wata tawagar yan Najeriya zuwa taron matasa na majalisar dinkin Duniya.

- Shi kuwa Angonta, Abolaji Abiola Ajibola kwararren jami’in gudanarwa ne mai shekaru 29, kuma yana aiki ne a kasar Ingila.

- Shima ya karanci alakar kasashen duniya, amma a kwalejin sarakai dake birnin Landan.

- Abolaji ma dan gwagwarmayan kare hakkokin bil adama ne

- A watan satumbar shekarar 2017 ne dai Abolaji ya nemi auren Fatima.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng