Ba na tsoron shiga kurkuku, zan ci gaba da fadin gaskiya da sukar gwamnati - Melaye

Ba na tsoron shiga kurkuku, zan ci gaba da fadin gaskiya da sukar gwamnati - Melaye

A ranar Talatar da ta gabata ne, sanata mai wakilcin jihar Kogi ta Yamma, Sanata Dino Melaye ya bayyana cewa, ba bu gudu ba bu ja da baya dangane da karar sa da gwamnatin tarayya ta yi, inda yake cewa zai ci gaba da suka tare da fadin gaskiya kan kowace gwamnati.

Melaye yake cewa, koda kuwa gwamnatin shugaba Buhari ce aka same ta da wani nakasu, ba zai kame bakin sa ya yi shiru ba, inda yake cewa ya lashi takobbi akan faduwar gaba ta jefa shi gidan kurkuku.

Ku tuna cewa, tun a watan Afrilun 2017, Sanata Melaye ya janyo hankalin al'umma kan yunkurin da aka yi na yi masa kisan gilla da Edward David ya nufata, wanda shine shugaban ma'aikata na gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello, wanda ya shigar da rahoto zuwa hukumar 'yan sanda.

Sanata Dino Melaye
Sanata Dino Melaye

A sakamakon wannan tuhuma da Melaye yake yiwa shugaban ma'aikata na gwamnatin jihar Kogi, gwamnati a ranar Lahadin da ta gabata take cewa wannan ba wani abu bane face kage.

KARANTA KUMA: Hotunan ganawar shugaba Buhari da tsohon shugaba Abdulsalami

Sai dai sanatan yace yana kan bakan sa na ci gaba da fadin gaskiya kan kowace gwamnati tare da caccakar ta muddin ta yi ba daidai ba.

Yake cewa, "na lashi takobbi akan fargaba na shiga gidan kurkuku, domin sai da na shiga gidan yari har sau 14 a lokacin gwamnatin Jonathan, hakazalika gwamnatocin Abacha da Babangida. Saboda haka bana shayin a jefa ni gidan kaso, don daman an gina sa ne saboda mutane, amma indai gaskiya ce yanzu muka fara fadenta."

Legit.ng ta kuma ruwaito cewa, a ranar talatar da ta gabata ne tsohon shugaban kasa, Abdulsalami Abubakar, ya yi ganawar sirrance da shugaba Buhari a fadar sa dake babban birnin kasar nan.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng