Ka daina shisshigi cikin al’amuran jihar Benue - Ortom ya gargadi Lalong
Rikicin tsakanin gwamnan jihar Benuwe, Samuel Ortom da takwaransa na jihar Flato, Simon Lalong ya dau sabon salo.
Gwamna Ortom ya bada wannan gargadi ne a ranan Litini, 12 ga watan Fabrairu a wani taron masu ruwa da tsaki karkashin jagorancin gwamnan jihar Ebonyin, David Umahi.
An fara ganawar tun ranan Lahadi amma sai ranan Litinin aka samu karashe tattaunawa a gari Makurdi, jihar Benue.
Gwamna Ortom ya bayyana cewa mataimakinsa, Benson Abounou ya hadu da Lalong kwanakin nan kuma Lalong ya jaddada cewa lallai ya gargadi Ortom a kan dokar hana kiwo.
Game da cewar Ortom, “ Mataimakina ya bayyana mini cewa sun tattauna da Lalong a wani taro inda ya ce kawai ya bada hakuri ne don yawan harsuna akana, amma lallai yana kan furucinsa na farko.”
“Ni ne gwamna a nan, ta yaya zai ce ya gargadeni, wanene shi ya gargade ni, sai dai ya bani shawara. Ka fadawa maigidanka ya daina shisshigi cikin al’amuran jihata.”
KU KARANTA: Rundunar sojin Najeriya sun fitittiki yan Boko Haram a Sabil Huda, sun ceto mata da yara
Zaki tuna cewa kwanakin baya gwamnan jihar Flato ya bayyana a fadar shugaban kasa cewa ya gargadi gwamnan jihar Benue a kan kafa dokan hana makiyaya kiwo a fili amma bai saurareshi ba.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng