Farfesa Wole Soyinka ya bayyana shugaba Buhari a matsayin marar kuzari a mulkin kasar nan

Farfesa Wole Soyinka ya bayyana shugaba Buhari a matsayin marar kuzari a mulkin kasar nan

- An bayyana shugaba Buhari a matsayin wanda baya tabuka komai a mulkin kasar nan

- Farfesa Wole Soyinka ya bayyana hakan a wata ganawa da yayi da manema labarai

- Ya bukaci shugaba Buhari da ya zage dantse domin ganin ya kawo karshen matsalolin da ake samu a gwamnatin sa

Farfesa Wole Soyinka ya bayyana shugaba Buhari a matsayin marar kuzari a mulkin kasar nan
Farfesa Wole Soyinka ya bayyana shugaba Buhari a matsayin marar kuzari a mulkin kasar nan

Dattijon marubucin nan, Farfesa Wole Soyinka, ya bayyana Shugaba Muhammadu Buhari a matsayin marar kuzari a tsarin tafiyar da mulkin Najeriya. Mista Soyinka wanda ya nuna takaicin sa game da halin da shugaban kasar yake ciki da kuma yanda gwamnatin sa take tafiyar da mulkin kasar.

DUBA WANNAN: 'Yan sanda sunyi nasarar kwato wasu makiyaya da shanu daga hannun 'yan kungiyar boko haram

Ya bayyana hakan ne a wani jawabi da yayi ga manema labarai, game da hare - haren da makiyaya suke kaiwa a yankunan manoma a kasar nan.

Da aka tambayeshi mai zai cewa Shugaba Buhari inda ace zasu hadu, Mista Soyinka ya amsa ya ce: "Zan ce Shugaba Buhari, ina tsamanin kana cikin damuwa akan lamuran kasar nan," inji shi.

Ana ta samun cigaban kurakurai a kasar nan, sannan kuma har yanzu ba wani kwakkwaran mataki da ake dauka, ya kara da cewa. Mista Soyinka ya bukaci Shugaba Buhari da ya tuna da lokacin da aka dakatar da Babban Sakataren hukumar lafiya na National Health Insurance Scheme (NHIS), Usman Yusuf, a matsayin daya daga cikin misalan kuskuran da gwamnatin sa ta yi.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng