Ina tsoron fushin ubangiji – Inji wani babban Fasto da ke neman yan mata da Mata mabiyansa
Wani matashin Fasto, Oluwasanjo Eniola ya dirka ma wata yar Cocinsa ciki, wai don ya bata ma matarsa rai, wanda a sakamakon haka aka samu haihuwar da namiji, inji rahoton Daily Trust.
Fasto Eniola da kansa ya shaida ma wata Kotun majistri wannan, ind aya bukaci kotun ta raba aurensa da matarsa, Basir, wanda yace bata bashi kukawar da ta dace, kuma bata kaunar aikinsa na Fastonci.
KU KARANTA: Kaico! An gano gawar wani Dansanda a jihar Benuwe, wanda yayi ɓatan dabo
“Ya Alkali mai shari’a, mata ta bata kaunar aikin da nake yi, sai dai kullum ta dinga fitina ta, haka zalika tana yawan damuwana kan yan mata da mata mabiyana, amma na sha fada mata cewar matan suna bani shawarar da bata bani.
“Ta taba tafiya Legas ba tare da izini na ba, ni kuma sai na koma wajen wata mabiyata, inda muka sadu da juna, har aka samu yaro namiji, amma bamu dade ban a yanke alakar mu, don gudun fushin ubangiji, don haka Kotu ta raba mu, don na fuskanci aikina na Fasto da kyau.” Inji shi.
Da take kare kanta, Basira ta roki Kotu da kada ta raba auren, “Na san na takura masa, musamman saboda alakarsa da matan Cocinsa, ina bukatar kotu ta bamu lokaci mu sulhunta kan mu, don kuwa bazan iya aure ba da yaya hudu,”
Daga nan sai Alkalin Kotun, Cif Ramoh Olafenwa y adage sauraron karar zuwa ranar 28 ga watan Feburairu, sa’annan ya shawarce su dasu sulhunta kansu ko dan yayansu.
Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
ko a http://twitter.com/naijcomhausa
KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng