Nigerian news All categories All tags
Bari ba shegiya ba ce: An tattake wasu motocin alfarma da aka shigo da su ta barauniyar hanya (Bidiyo)

Bari ba shegiya ba ce: An tattake wasu motocin alfarma da aka shigo da su ta barauniyar hanya (Bidiyo)

- An dagargaza motocin alfarma da aka yi fataucinsu

- Wata katuwar mota ta hau kan motocin na alfarma, ta tattake su, ta murkushe su

Wani abin ban mamaki da daure kai ya faru a kasar Philippines, inda gwamnatin kasar ta bada umarnin a nike duk wasu motoci da aka shigo da su kasar ta hanyar fasa kauri, inji rahoton Muryar Amurka, VOA.

Wannan aiki na musamman ya faru ne a ranar Litinin 12 ga watan Feburairu, inda wata katuwar mota ta hau kan motocin na alfarma, ta tattake su, ta murkushe su, tare da dagargaza su ba tare da kula da alfarmarsu ba.

KU KARANTA: Yayan jam’iyyar APC APC sun gudanar da zanga zanga sakamakon mulkin kama karya

Shugaban kasar, Rodrigo Duterte ne da kansa ya bayar da umarnin gudanar da wannan aiki, wanda ya bayyana shi a matsayin kashedi ga masu safarar kaya zuwa kasar ta barauniyar hanya, ba tare da bin doka da ka’ida ba.

Duterte yace an dade ana gudanar da wannan aiki na fasa kauri a kasar, shekara da shekaru, amma gwamnatinsa ba za ta lamunci karya doka da oda ba, kamar yadda majiyar Legit.ng, ta jiyo.

A wani labarin kuma, hukumar fasa kauri ta Najeriya ta samar da kwale kwale na zamani don yaki da masu kautar da man fetir daga Najeriya zuwa makwabtan kasashen Najeriya.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel