Nigerian news All categories All tags
Kotu ta kwace fasfo din tsohuwar minista da ake tuhuma da badakalar wawure miliyan N450m

Kotu ta kwace fasfo din tsohuwar minista da ake tuhuma da badakalar wawure miliyan N450m

- Wata kotu mai zamanta a Jos, babban birnin jihar Filato, ta kwace fasfo din tsohuwar minista, uwargida Sarah Reng Ochekpe

- Ana tuhumar tsohuwar ministar albarkatun ruwa Sarah Reng Ochekpe da safarar miliyan N450m

- Hukumar EFCC, mai yaki da cin hanci da rashawa, ce ta gurfanar da tsohuwar ministar da wasu mutane biyu

Wata kotun Najeriya mai zamanta a garin Jos, babban birnin jihar Filato, ta kwace fasfo din tsohuwar ministar albarkatun ruwa, Sarah Reng Ochekpe, da wasu mutane biyu da ake tuhuma da laifin cin hanci.

A wata takardar kara FHC/J/141C/2017 da hukumar EFCC, mai yaki da cin hanci da rashawa, ta gabatar gaban kotun a jihar Filato, ta zargi tsohuwar ministar da wasu mutane biyu; Raymond Dabo da kuma shugaban yakin neman zaben tsohon shugaban kasa Jonathan, Leo-Sunday Jitong, da laifin almundahanar kudi da yawansu ya kai miliyan N450m.

Kotu ta kwace fasfo din tsohon minista da ake tuhuma da badakalar wawure miliyan N450m

Tsohuwar minista, Sarah Reng Ochekpe

A zaman kotun na farko, mai shari'a Musa Kurya, ya bayar da belin wanda ake bisa la'akari da kimar su.

A yayin zaman kotun na yau, hukumar EFCC ta hannun lauyanta, Ahmad Yakubu Muntaka, ta canja cajin da take yiwa tsohuwar ministar da ragowar mutanen biyu daga guda biyu zuwa uku.

DUBA WANNAN: Hukumar EFCC ta shiga maganar batan miliyan N36m da 'wai' maciji ya hadiye

Wadanda ake tuhumar, ta bakin lauyansu, sun musanta zargin da hukumar EFCC ke yi masu tare da neman kotu ta sake bayar da su beli.

Mai shari'a Musa Kurya ya bukaci wadanda ake tuhumar da su bayar da hotunan su tare da ajiye fasfo dinsu kafin daga bisani ya daga ci gaba da sauraron karar zuwa gobe, Laraba.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel